✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya na cikin kasashen da ake gallaza wa yara – UNICEF

Asusun UNICEF ya ce akwai kuma kananan yara fiye da 2, 200 da aka yi wa fyade.

Wani rahoto ya ce a cikin shekara biyar, kananan yara fiye da dubu 21 ne Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar an dauke su aiki a matsayin mayaka a Afirka ta Yamma da Afirka ta Tsakiya.

Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya gano cewa daga shekarar 2016, yankin Afirka ta Yamma da na Tsakiya sun samun adadi mafi yawa na rahotannin da Majalisar Dinkin Duniya ta tantance kan gagarumin take hakkin kananan yara a lokacin rikice-rikice.

Rahoton na UNICEF ya zargi dakarun tsaro da kungiyoyi masu gwagwarmaya da makamai da ci da gumin kananan yara a yankunan biyu.

Asusun UNICEF ya ce bayan kananan yara sama da dubu 21 da aka dauka a matsayin mayaka akwai kuma kananan yara fiye da 2, 200 da aka yi wa fyade.

An kuma sace kananan yara sama da 3,500, sannan an kai hari 1,500 a kan makarantu da asibitoci a Afirka ta Yamma da Afirka ta Tsakiya a cikin shekara biyar din da suka wuce.

Rahoton ya ce a Najeriya an kai hare-hare 25 a kan makarantu, inda aka sace ɗalibai fiye da 1,400.

A cewar rahoton rikicin da ya yi kamari a Arewa maso Gabashin Najeriya a tsawon shekara 12 yanzu, ya zama sanadin kashe dubban yara da nakasa wadansu da sacewa da raba wadansu da gidajen iyayensu, baya ga wadanda aka keta wa hakki.

UNICEF ta ce tun shekarar 2005, daya daga cikin hudu na wani gagarumin take hakkin kananan yara da aka samu a duniya, an aikata shi ne a Afirka ta Yamma ko Afirka ta Tsakiya.

Rahoton ya ce a bara kananan yara sama da 6, 400 ne aka keta wa hakki a yankunan Afirka, wanda a cikinsu kashi 32 cikin 100 ’yan mata ne.

Babbar Jami’ar UNICEF a Maiduguri Phuong T. Nguyen ta ce kananan yaran Najeriya ko dai kai-tsaye an kai musu hari ko tsautsayi ya rutsa da su a wani hari, sanadiyyar tabarbarewar tsaro da ake ci gaba da gani a fadin kasar nan, kamar yadda BBC ya ruwaito.

A cewarta, wannan ba abu ne da za a lamunta ba, inda ta ce, “Wannan muhimmin rahoto ya nuna tsananin keta hakkin kananan yara a Najeriya da Afirka ta Yamma da Afirka ta Tsakiya. Lamarin da ta ce dole ne dukkan bangarori su kawo karshensa.

Ta ce, “Wajibi ne, kananan yara su samu zarafin girma, su yi ilimi, su samu aikin yi, kuma su ba da gudunmawarsu ga kyakkyawar makomar wannan kasa.”

“Hakan kuma zai samu ne kawai idan an kare kananan yara daga tarzoma da kuma mummunan tasirin rikice-rikice,” inji ta.

Rahoton ya kuma nuna cewa manyan matsalolin jinkai na ci gaba da faruwa a Afirka ta Yamma da Afirka ta Tsakiya.

“Abin da yake faruwa a Kamaru da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango da matsalolin da ke bukatar daukin gaggawa a tsakanin kasashe ciki har da rikice-rikice a Tsakiyar yankin Sahel da yankin Tafkin Chadi na da gagarumar illa ga rayuwar kananan yara da al’ummomi,” inji rahoton.