Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo, ya ce Najeriya na bukatar shugaba mai kishi da kuma dan tabin hankali don dora kasar nan kan turba mai kyau.
Obasanjo, ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin mai neman takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar PDP, Mohammed Hayatu-Deen, a gidansa da ke Abeokuta, a Jihar Ogun ranar Alhamis.
- Zan yi amfani da fasahar zamani wajen magance matsalar tsaro — Saraki
- Murtala Garo: Dan takarar Ganduje na shirin ficewa daga APC
Ya koka kan halin da ake ciki a Najeriya, inda ya dora alhakin da ake ciki ga kansa da kuma sauran ’yan Najeriya da ke son ganin kasar ta inganta.
Tsohon Shugaban Kasar ya ce Najeriya za ta iya shawo kan matsalolin tsaro a cikin shekara biyu tare da shugaban da zai iya yanke hukunci mai tsauri.
Don haka ya bukaci ’yan Najeriya da su jajirce su kuma kasance a shirye wajen sadaukar da abubuwa don mayar da kasar kan turba mai kyau.
Ya ce “Wasu mutane sun ce tunanin ’yan Adam gajere ne, watakila sun yi daidai domin idan tunanin ’yan Adam ba gajare bane, da ba mu aikata wasu kura-kuran ba.
“Halin da ake ciki abu ne mai ban tsoro. Ina so in jaddada cewa, halin da Nijeriya ke ciki, mummuna ne, sai ’yan Najeriya sun mun daidaita al’amura suke. Don haka ‘yan Najeriya su jajirce wajen yin abin da ya kamata a yi domin mayar da kasar nan kan turba mai kyau.
“Kuma ka yi gaskiya da ka ce duk inda ka je yanzu, daya daga cikin abin da ka ji shi ne Najeriya ba ta kan saiti, amma me zai hana Najeriya ta hawa kan saiti?
“Zan fadi abubuwa hudu, wadanda aka tuna min da su a safiyar yau. Daya shi ne ilimi. Idan Najeriya ba ta kan saiti, kila ilimin da ya kamata mu samu ba shi da inganci, ta yadda za mu san nahiyarmu da ma duniya, idan wannan ilimin na da inganci, za mu yi abin da ya dace, a lokacin da ya dace.
“Na biyu shi ne hangen nesa, mene ne hangen nesa da mu ke da shi? Za ka iya zama mai idanu amma ka kasance makaho. Kuma na yi imani wannan shi ne cikin halin da mu ke ciki.
“Na uku shi ne kuduri, yana da kyau mutum ya kasance mai kudurin abin da ya ke son cim ma, saboda duk inda na je bani da inda ya kai Najeriya, kuma a ko ina zan iya bugar kirji na ce daga nan na fito.
“Sai ka kasance mai hauka a game da abin da kake so, idan na dubi (Hayatu-Deen) na ce eh, kai ma ka haukace a kan Najeriya,” inji Obasanjo.
Tun da farko a cikin jawabin nasa, Hayatu-Deen ya bayyana cewa Najeriya na samun koma baya da lalacewar abubuwa cikin sauri.
Hayatu-Deen, wanda tsohon Shugaban Bankin Kasa da Kasa na FSB ne, ya gana da daliget din jam’iyyar PDP a sakatariyar jam’iyyar da ke Abeokuta.