Najeriya ta yi rashin nasarar zuwa Gasar Kofin Duniya da za a gudanar a kasar Qatar, bayan yin kunnen doki da kasar Ghana.
Ghana ta samu nasarar zuwa gasar ce sakamakon jefa kwallo daya mai ban haushi a ragar Najeriya.
- Harin jirgin kasa: Har yanzu muna cigiyar mutane da dama – Gwamnatin Kaduna
- Na kadu matuka da harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna — Buhari
Tawagar Black Star ta kasar Ghana ce ta fara zura wa Super Eagles ta Najeriya kwallo a minti na 10 ta hannun dan wasanta Thomas Partey, yayin da kuma kaftin din Super Eagles, Troost-Ekong ya farke kwallon a minti na 22 daga bugun fenareti.
Dan wasan gaban Super Eagles, Victor Osimhen ya zura kwallo a minti na 34, amma na’urar VAR ta kashe kwallon inda aka ce ya yi satar gida.
A makon da ya gabata, Najeriya ta fafata wasan farko da Ghana a birnin Kumasi, amma aka tashi wasan babu ci.
Tawagar ’yan wasan Najeriya ta mamaye wasan da kashi 62, yayin da Ghana ke da 38.
Super Eagles ta yi bugu 20, wanda 15 daga ciki suka yi fadi sannan biyar daga ciki suka zamo mafi hatsari.
An buga wasan a filin wasan na M.K.O Abiola da ke Babban Birnin Tarayya Abuja, inda aka samu dandazon magoya fiye da 60,000.