✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ce kasa ta 114 mafi samar wa ’yan kasa jin dadi a duniya —MDD

Kasar Finland ta ci gaba da rike matsayin na daya tsawon shekara hudu.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana Najeriya a matsayi na 114 daga cikin jerin kasashe 146 da ‘yan kasar suka fi jin dadi.

Uganda ce ke bin baya, yayin da Tanzaniya da Kenya ke take mata baya a jerin kasashen.

Kenya ce ke matsayi na 119, wanda hakan ke nufin ta kara yin kasa daga matsayi na 86 a shekarar da ta gabata, yayin da ita kuma Uganda take kasa da Kenya a shekarar da ta gabata da mataki biyu inda take matsayi na 83 .

Tanzaniya ta lula matsayi na 134 daga na 94 da take a baya.

Tsubirin Mauritius shi ne na daya cikin jerin kasashen Afrika da mutanensu suka fi jin dadi, yayin da a bara take matsayi na 44 a duniya.

A jerin sunayen da majalisar ta fitar, Ruwanda ce kasa ta karshe da mutanenta suke da karancin jin dadi, inda a da take matsayi na 147.

Sai dai sunan Sudan da kasar Burundi ya yi batan-dabo daga cikin jerin sunayen da majalisar ta fitar, wato ba sa daga cikin sunayen kasashen da ta fitar.

Ita kuwa kasar Finland, ita ce ke matsayi na daya a duniya cikin shekara hudu a jere, yayin da Denmark, Switzerland, Iceland da kuma Netherlands ke biye mata a baya.