Mutane miliyan 70 da ke sayen kayan masarufi na yau da kullum shi ya sa Najeriya ta zama gagara-gasar kasuwannin Afirka.
Babban jami’in kamfanin inshora ta Old-Mutual, Mista Zomunoda Chizura ya faxi haka a bukin buxe ofishin kamfanin a cikin gidan Murjanatu, kan titin Zambezi a birnin Abuja, bayan a da suna zaune ne a cikin bankin Eco.
Ya ce yawan al’umma masu kasuwanci a Najeriya ya fi yin kasuwanci a qasar Ghana da kuma Afirka ta Kudu dungurungun.
Ya qara da cewa, “Kamfanin Inshora na Old Mutual an kafa shi ne a shekaru 171 da suka shuxe a qasar Afirka ta Kudu. Kuma sun fara kasuwansi ne a Najeriya kusan shekaru 10 da ma’aikata 80, inda a yanzu suna da ma’aikata kusan 500 da rassa a manyan biranen qasar nan. Muna kuma zuba jari ne lokacin da kasuwa take cikin matsi ta fadi, da burin za mu ci riba a nan gaba in harkan tattalin arziki ta warware.”
Mista Chizura ya qara da cewa Inshora tana kare xan kasuwa daga rage asara lokacin da aka samu akasi a kasuwa. Ya kuma yaba wa Najeriay ganin yadda jama’a da dama suke yin inshora inda ya sa kamfanin ta Old-Mutual take dagawa daga mataki na tsakiya tsakanin kamfanonin inshora zuwa burin zama cikin manya-manyan na gaba kaxan.
‘Najeriya ce babbar kasuwa a Afirka’
Mutane miliyan 70 da ke sayen kayan masarufi na yau da kullum shi ya sa Najeriya ta zama gagara-gasar kasuwannin Afirka.Babban jami’in kamfanin inshora ta…
