✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ba za ta taba samun zaman lafiya sai… Sanata Ndume

Shugaban Kwamitin Sojojin Kasa a Majalisar Dattawa, Sanata Ali Muhammad Ndume na Jam’iyyar APC daga Kudancin Borno, ya bayyana damuwarsa game da yadda ya ce…

Shugaban Kwamitin Sojojin Kasa a Majalisar Dattawa, Sanata Ali Muhammad Ndume na Jam’iyyar APC daga Kudancin Borno, ya bayyana damuwarsa game da yadda ya ce ake aikata ba daidai ba wajen daukar aiki a ma’aikatu da hukumomin Gwamnatin Tarayya, inda ya ce lokaci ya yi da za a taka wa lamarin birki kuma a haramta shi.

Ya ce galibin ’yan Najeriya da ba su da ido da kwalli ba sa samun ayyuka a ma’aikatun Gwamnatin Tarayya,  “babban shamakin da ke hana su, shi ne ba su san kowa ba a wuraren,” inji shi.

Ya ce: “Najeriya za ta zauna lafiya ne kawai idan aka ce dan talakan da bai san kowa ba, zai iya zama wani abu ba tare da wani babba ya san shi ba.”

Sanata Ndume ya fadi haka ne ga manema labarai a lokacin da yake bayani kan Kudirin Dokar Kafa Jami’ar Sojin Kasa ta Biyu a Jihar Borno,­­­  wanda ya tsallake karatu na biyu a zauren Majalisar Dattawan.

Ya ce: “A wasu lokutan masu neman aikin kan bayar da abin goro, sakamakon yadda suka zaku su samu aikin; sai dai hakan ba daidai ba ne sam.”

“Idan za su dauki mutane aiki; to ya kamata su dauke su aikin bisa turbar tanadin tsarin mulki da na tsarin rabon gurabe na daidaiton shiyyoyin siyasar kasar da kuma cancanta. Ina matukar takaicin abin sosai, lura da yadda na zama wani abu ba tare da na san wani ba. A yanzu da akwai wadansu ire-irena amma babban shamakinsu a nan shi ne ba su san kowa ba.

“Wannan abin takaici ne matuka. Kuma ina fadi cewa kasar nan ba za ta taba samun zaman lafiya ba, idan dai har dan talakan da bai san kowa ba kuma ba wanda ya san shi, ba zai iya  zama wani abu ba,”  inji shi.