Aki-bishop din cocin Darikar Katolika na Abuja ya gargadi shugabannin kasar nan kan yadda suka sa kasar ta zama ‘marar dadin zama’ ga matasa, lamarin da ke sa matasan suke kaura zuwa kasashen Turai.
Kadinal John Onaiyekan ya ce in da shi ne Shugaban Kasa zai yi murabus daga mukaminsa.
Ya soki jami’an gwamnati kan yadda suka mai da hankali wajen harkokin da suka shafe su, ta gina manyan gidaje da tafiye-tafiye zuwa kasashen duniya, maimakon kula da hakkokin jama’a.
Aki-bishop din, mai shekara 75 ya ce yana jin kunyar yadda za ka ga mata ’yan Najeriya suna gararamba a kan tituna a birnin Rum da sauran birane na kasar Italiya. Kadinal Onaiyekan ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da manema labarai gabanin wani taro da za a gudanar a wani coci don tattauna yadda za a magance matsalar yawan zuwa ci-rani da aka gudanar a Abuja ranar Talatar da ta gabata.
“Ina gaya muku balo-balo cewa ina jin kunya sosai a matsayina, na babban Kadinal daga Abuja. Idan ina tafiya a titunan Rum da Milan da Niples in ga ’ya’yanmu mata suna gararamba a kan titunan suna sayar da jikinsu,” Kadinal din ya shaida wa BBC, bayan taron manema labaran.
“Na ji kunya kuma na tsaya har na gayar da wadansu daga cikinsu – ba za ka iya tattaunawa da su ba, saboda akasari an kawo su ne daga kauyuka ba su yi karatu ba. Abin da kawai suka sani shi ne, kawai abin da aka kawo su, su yi shi ne karuwanci- na ji kunya.”
Babban Bishop din ya yi tir da ’yan siyasar kasar nan, inda ya ce idan ba su da wata manufa a kan ci gaban kasar nan da samar da tsaro kamata ya yi kada su shiga cikin harkokin siyasa.
Sai ya yi kira ga gwamnati ta “gyara Najeriya,” hakan zai sa maimakon matasa su rika yin kaura, sai a samu masu zuwa yawon bude-ido zuwa Nahiyar Afirka ta Yamma, kuma ’yan Najeriya su iya fita cikin martaba da daraja.