Uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu, ta ce ba za a ayyana Najeriya a matsayin matalauciyar kasa ba duk da irin matsalolin da ta ke fuskanta.
Sai dai ta yi kira ga masu hannu da shuni da su taimaka wa talakawa. .
- Yadda Aka Fara Gasar Alkur’ani ta Kasa Karo Na 38 A Yobe
- Matsahi ya kashe abokinsa saboda na’urar jin sauti a Kano
A sakonta na Kirsimeti a gidan marayu na Nana Berry da ke Abuja, ta ce 2024 za ta zama shekara mai cike da alfahari ga ‘yan Najeriya.
Ta ce, “Yayin da muke shiga shekara ta 2024, ya kamata sakonmu ya zama yadda zai sauya rayuwar matasa.
“Ya kamata mu daina maganar talauci a gaban ’ya’yanmu, mu ba talakawa ba ne, masu hannu da shuni su ma su kula da talakawa su taimake su, shi ke nan abin da ake bukata.
“Mun cire batun talauci daga cikin al’amuranmu saboda yana gurbata zukatan matasa. Za mu shiga shekara mai cike da fata nagari.”
Uwargidan shugaban kasar ta shawarci iyaye da su rungumi dabi’ar koyar da yaransu kyawawan dabi’u don su zama manya nagari.