More Podcasts
Domin sauke shirin latsa nan
Tsadar gidajen haya a Abuja ta sa yawancin mazauna birnin kan shafe shekara a koyaushe suna fadi-tashin tara abin da za su biya kudin haya.
Duk da haka, wasu masu gidaje a birnin ba sa karbar kudin haya sai na shekara biyu zuwa sama.
A kan haka ne Majalisar Dattawa ta fara aikin kafa dokar wajabta biyan kudin haya wata-wata a Abuja, maimakon shekara-shekara.
’Yan hayar Abuja sun bayyana wa shirin Najeriya A Yau yadda suke ji idan lokacinsu na biyan haya ya karato.
Akwai kuma bayanin abin da dokar ta kunsa, shin za ta yi aiki, kuma wa za ta amfana tsakanin ’yan haya da masu gidajen haya?