More Podcasts
Kula da lafiya na nufin yin abubuwa da ke kare mutum daga kamuwa da cututtuka da kuma tabbatar da cewa jiki na aiki yadda ya kamata.
Wannan ya haɗa da cin abinci mai gina jiki, motsa jiki akai-akai, da dai sauran su.
Sai dai a wannan zamani ’yan Najeriya ba kasafai suke kula da lafiyar jikinsu ba, a mafi yawan lokuta ma sai ciwo ya kwantar da mutum sannan yake tunawa da likita.
Ko waɗanne matakai ya kamata al’umma su ringa dauka wajen kare kansu da kuma lafiyar jikinsu?
- NAJERIYA A YAU: Mece ce Makomar Dimokuraɗiyya Idan Aka Wajabta Kada Kuri’a?
- DAGA LARABA: Tasirin Mulkin Karɓa-Karɓa A Najeriya
Shirin Najeriya A YAU na wannan lokaci zai yi nazari ne kan yadda al’umma za su dinga kula da lafiyar jikinsu.
Domin sauke shirin, latsa nan