Domin sauke shirin, latsa nan
A yayin da matsaloli da zargin magudi ke ci gaba da mamaye zabukan fitar da ’yan takara da na shugabannin jam’iyya da sauransu a Najeriya, wane tsarin zabe ne ya fi dacewa?
Majalisar Dokokin kasar na kokarin yi gyara dokar zabe ta yadda kowa zai samu shiga an dama da shi a zaben shugabanni; amma kuma ra’ayoyin ’yan Najeriya sun bambanta game da komawa amfani da tsarin ’yan tinke ko amfani da daliget.
Shirin Najeriya a Yau na wannan karon ya yi dubi ne a kan amfani da tsarin ’yan tinke ko zaben daliget da kuma wanda a cikinsu kwalliya za ta biya kudin sabulu.
A yi sauraro lafiya.