More Podcasts
A kwanakin baya ne dai Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙirƙiro sababbin hukumomin raya shiyyoyin ƙasar nan da nufin kawo musu ci-gaba.
Gabanin ƙirƙirar waɗannan hukumomin, gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ce ta fara kirkirar hukumar raya yankin Neja Delta bayan wasu ƙalubale da suka dabaibaye yankin.
Na baya-bayan nan ita ce Hukumar Raya yankin Arewa ta Tsakiyar ƙasar nan bayan da ’yan yankin suka nace da yin ƙorafin cewa an mayar da su saniyar ware.
- NAJERIYA A YAU: Dalilan Saukar Farashin Kayan Masarufi A Kaswanni
- DAGA LARABA: Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar Hausa
Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan irin ci-gaban da waɗannan hukumomin raya shiyyoyi za su samar ga al’ummar ƙasa.
Domin sauke shirin, latsa nan