✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

NAJERIYA A YAU: Manyan Dalilan da Suka Sa aka zabi Abdullahi Adamu Shugaban APC

Dalilan da shugaba Buhari ya amince da nadin Abdullahi Adamu a matsayin jagora.

More Podcasts

Domin sauke shirin latsa nan

Zaben tsohon gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Abdullahi Adamu a matsayin shugaban jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ya bar tambayoyi da yawa a cikin zukatan jama’a.

Ganin cewa Abdullahi Adamu na daya daga cikin wadanda su ka kafa jam’iyyar PDP, ya yi gwamna sau biyu a karkashin inuwar  PDP, ya taba zama sakataren kwamitin amintattu a PDP.

Wadanne dalilai ne suka sa har shugaba Buhari ya amince da nadin Abdullahi Adamu a matsayin jagora?