✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nagari na kowa

Assalamu alaikum,wannan sati in Allah ya yarda za mu yi magana a kan ladubban da ya kamata uwa ta dora yaro a kai tun kafin…

Assalamu alaikum,wannan sati in Allah ya yarda za mu yi magana a kan ladubban da ya kamata uwa ta dora yaro a kai tun kafin ya fara magana har zuwa lokacin da ya zai fara buda baki.

Kafin mu shiga bayani yana da kyau mu kara jaddada muhimmancin ilimi ga ’ya mace.Domin kuwa idan mace ba ta da ilimi akwai matsala babba. Da wuya ta iya tarbiyyar yara yadda ya kamata har su zama abin alfahari ga kawunansu da iyayensu da ma al ’umma baki daya.Sai dai a duk lokacin da ake zancen ilimin ’ya mace,ba ya nufin ’ yan maza su je su yi ta barci,a’a kowa da kowa ya tashi ya nemi ilimi domin a gudu tare a tsira tare,domin kuwa wata rana su ne za su zama iyaye. Iyaye kuwa su ne malamai na farko da suke da matukar tasiri ga rayuwar yaro. Musamman uwa,domin ita ce cikin ikon Allah take rainon yaro tun daga haihuwarsa ,har ta fara koya masa zama har ya fara rarrafe daga nan sai tsayuwa har dai ta koya masa tafiya da magana da sauransu.Kuma ita ce jigon tarbiyya, don haka muka kawo wasu daga hanyoyin da suka kamata a bi,domin taimaka wa yaro ya zama Nagari.
-Duk lokacin da yaro ya tashi daga barci ki yi kokkarin karanta masa addu’ar tashi daga barci.Idan ya nufo ki sai ki yi masa sallama cikin farin ciki da annashuwa.Kada ki nuna masa ke ‘yar boko ce, ki ce masa “Hello” ko “Hi” ko “ Good morning”.Wannan zai taimaka masa ya tashi da sanin muhimmancin sallama.
-Idan za ki dauki shi ki ambaci Allah ,haka idan za ki ajjiye shi.
-Duk lokacin da zai ci, ya sha, ki ce “Bismillah” idan ya gama ki ce “Alhamdulillah”.Da zarar ya fara magana ki koya masa ya fada da bakinsa.
-Duk lokacin da yaro ya fadi ko ya buge kada ki yi ihu,maimakon haka ki yi sauri ki ambaci Allah.Wannan zai sa tun yana karami ya san ambaton Allah cikin wuya ko dadi.
-Idan ya yi atishawa kada ki yi tsaki,maimakon haka ki ce “Alhamdulillahi”.
-Lokacin da yaro zai yi barci,ki rika karanta masa kur’ani ko ki kunna masa karatun kur’ani.Ki guji kunna wa yaro kade-kade da wakokin shirme domin nisanta shi daga shaidanu tun yana dan karami.
-Idan zai shiga ban daki, ki karanta masa addu’ar shiga,kuma ki nuna masa ya shiga da hagu sannan ya fito da kafar dama.
-Haka nan idan za ki cire ko saka masa kaya ki yi addu’a,domin nisanta shi daga shaidan.
-Hatta saka takalmi ki nuna masa farawa da kafar dama bayan fadin bismillahi.
-Ki zauna da yaronki kamar tsawon awa daya kuna sauraron karatun al kur’ani tare,domin ya san muhimmancin kur’ani.Kuma wannan yana taimakawa wajen sanya nutsuwa a cikin zukatanku.
-Kada ki rika zagin yaro,duk lokacin da ya dame ki da koke-koke ko kiriniya da rashin ji, ki rika cewa “Allah ya shirye ka”.Kada ki bari ranki ya yi mugun baci ki rika dukansa ko ki yi masa mummunar addu’a.Ki tuna Hausawa suna cewa “Yaro ba mutum ba, sai ya girma.”
Idan uwa ta daure ta dora yaronta a kan wannan tafarki,koda ya girma koyon wadannan addu’oi ba za su yi masa wahala ba.Kuma da wuya shaidanu su yi tasiri a kansa balle ya zama gagararre,yadda kowa zai guje shi, domin kuwa ana cewa “Nagari na kowa,mugu sai mai shi.”
Allah ya taimaka mana a bisa tarbiyyar ’ya’yanmu domin su zama ’ya’ya nagari kuma abin alfahari ga kowa.