✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Na zabi sana’ar ruwaya ne saboda kalubalen da ke cikinta’

Wani matashi da ke sana’ar gyaran wutar lantarkin mota ‘ruwaya’, mai suna Aminu Salisu, dan kimanin shekara 22, ya ce ya zabi sana’ar ne a…

Wani matashi da ke sana’ar gyaran wutar lantarkin mota ‘ruwaya’, mai suna Aminu Salisu, dan kimanin shekara 22, ya ce ya zabi sana’ar ne a kan sauran sana’o’i saboda kalubalar da take cikinta.
Malam Aminu Salisu, dan asalin kauyen Makurdi da ke karamar Hukumar Bakori a Jihar Katsina, ya bayyana wa Aminiya haka a wata tattaunawa da suka yi, kuma ya kara da cewa sana’a ce da ke bukatar kaifin basira.
Ya ce, “Ba kamar sauran sana’o’i ba, ita sana’ar gyaran wayoyin mota, wacce muke kira ‘ruwaya’, sana’a ce da take tafiya tare da basira da kaifin kwakwalwa da kuma zurfin tunani. Shi ya sa take da kalubale da yawa. Sau da yawa za a kira ni a ce min haka kawai mota ta mutu ko kuma an tashe ta ta ki tashi, to ka ga a wannan lokacin idan ba natsuwa ka yi ba, ka tara hankalinka wuri daya, ba za ka iya gano matsalar da ke damun motar ba. Wutar lantarkin mota tana da sarkakiya sosai saboda tarin wayoyi za ka gani a cukurkude, sai ka yi amfani da kaifin basira sannan ka iya gano wayar da take da matsala. Ka ga ni da kwakwalwata nake amfani, amma wadansu sai sun yi amfani da na’ura mai kwakwalwa sannan su iya gano abin da yake damun mota. Shi ya sa gyrana ruwayar mota ba kowa ke iya koya ba, sai mai fahimta da natsuwa, tunda ita mota ba magana za ta yi maka ba ta ce ga matsalar da ke damunta, kai za ka yi amfani da basirarka ka gano matsalar da ke damunta”.
Malam Aminu ya ce ya bar karatun bokon da yake yi ya je Legas ya kama sana’ar hannu ta koyon gyaran wutar mota saboda rashin wanda zai dauki nauyinsa kan haka. Sannan ya mayar da hankali a kan sana’ar gyaran wayoyin mota ne, musamman saboda mutuwar yayansa da ya kai shi Legas.
“Shi yake ciyar da ni. Yana mutuwa, sai rayuwa ta canja mini, abinci ya yanke mini, sai Allah Ya sa min tunanin dagewa kan koyon wannan sana’a don dogara da kaina”. Inji Aminu
Ya ce babu irin motar da baya gyarawa, cikin yardar Allah, amma ya fi kwarewa a kan sanfurin motar Toyota da Honda. “Sai dai abin da mutane ya kamata su sani, kowane ruwaya da irin samfurin motar da ya fi kwarewa a kai, saboda kowane kamfanin mota yana da tsarin yadda yake shirya wutar motarsa da kuma irin fasahar da ya yi amfani da ita”. Inji shi.
Dangane da rashin shiga sana’ar canji da mafi yawan Hausawa kan yi a Legas kuwa, sai ya ce, “Ban yi sha’awar canji ba, saboda sana’ar canji idan ba ka da mai taimaka maka, wahala za ka yi ta yi. Ita kuwa sana’ar da nake yi ba ta bukatar wani jari mai yawa, kwakwalwarka da karfinka su ne jarinka”.
Malam Aminu ya ce ya sami nasarori, wadanda suka hada da ciyar da kansa da tallafa wa iyayensa da kuma taimaka wa abokai da ’yan uwansa, kuma ya bayyana ba ya fuskantar wata matsala, saboda har yanzu yana koyon sana’ar ne a karkashin mai gidansa. Amma yana da burin idan ya sami dama, zai koma gida domin ya ci gaba da gudanar da sana’arsa.