✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Na yi mamaki da na ji an ce Salman Rushdie bai mutu ba – Wanda ya caka masa wuka

“Na tsani Salman kwata-kwata, sam ba na son ganinsa."

Matashin da ake zargi da daba wuka ga Salman Rushdie, mutumin da ya yi batanci ga Annabi Muhammad (S.A.W), Hadi Matar, ya ce ya yi matukar mamaki da jin cewa Salman din bai mutu ba bayan ya daba masa wukar.

Hadi dai, mai shekara 24, a baya ya musanta aikata laifin ta bakin lauyansa, kuma yanzu haka yana tsare a kurkukun gundumar Chautauqua da ke jihar New York ta Amurka.

Ana sa ran zai gurfara a gaban kotu ranar Juma’a.

Sai dai da yake zantawa da jaridar New York Post ta bidiyo daga kurkukun, Hadi ya ce, “Na cika da mamaki matuka lokacin da na jin labarin cewa Salman bai mutu ba.

Ya ce da farko dai ya yanke shawarar cewa wajen taron da aka yi a makarantar Chautauqua ne bayan ya ga sakon da Salman ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa shi ma zai je wajen.

“Na tsani mutumin nan kwata-kwata. Ba na tunanin mutumin kirki ne, sam ba na son ganinsa.

“Shi ne mutumin da ya yi batanci ga Musulunci da Musulmai,” inji Hadi.

Salman dai ya wallafa fitaccen littafinsa da ya yi wa lababi da The Satanic Verses a shekarar 1988, wanda ya kai ga Shugaban Addini na Iran, Ayatollah Khomeini ya bayar da fatawar a kashe shi a shekarar 1998.

Sai dai Hadi ya shaida wa New York Post cewa ’yan shafuka kadan ya karanta a cikin littafin, kuma ba zai iya tantance ko fatawar Ayatollah ta yi tasiri a zucuyarsa ba.