✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na yi da-na-sanin soyayya da Timaya – Ummi Zee Zee

Fitacciyar tsohuwar jarumar finar finan Kannywood, Ummi Zee Zee ta bayyana cewa babban abin da take yin da-na-sani a rayuwarta shi ne yadda ta yi…

Fitacciyar tsohuwar jarumar finar finan Kannywood, Ummi Zee Zee ta bayyana cewa babban abin da take yin da-na-sani a rayuwarta shi ne yadda ta yi soyayyar da shahararren mawakin nan na Kudu wato Timaya. 

Ummi Zee Zee ta bayyana haka ne a wata tattaunawa da ta yi da jaridar Daily Nigerian, “ An taba ruwaitowa cewa wai na bar Musulunci na koma wani addinin daban saboda alakata da Timaya. Na yi matukar mamakin jin wannan labarin. Labari ne kawai na kanzon Kurege da bai da tushe, sannan kuma an yi da nufin bata min suna. Har yanzu na kasa manta wannan lamarin. Ni mutum ce mai addini, ina son addinin Musulunci. Duk lokacin da na samu sarari, ina karanta hadisan Manzon Allah.

Zee Zee ta kara da cewa marigayi dan Ibro da marigayya Aisha dan Kano suna cikin wadanda take girmamawa a masana’antar fim  ta Kannywood.

Da aka tambayeta game da shirin aure, Zee zee sai ta tabbatar da cewa ta shirya yin aure, kuma tana tunanin za ta yi aure daga yanzu zuwa karshen shekara. 

Daga karshe da aka tambayet a maganar cewa arzikinta da ake ta yayawata duk karya ce kawai, sai ta ce, “ina da arziki sosai, don haka idan ma wani ya  mini kyautar wasu ’yan miliyoyi, ba zan yi murna ba kamar yadda ake tunani. Ina da wadata daidaib gwargwado. Har na saya wa ma’aikatana gidaje da motoci.”