✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Na yi asarar buhu 700 na shinkafa a ambaliya —Manomi

Na karbi bashi, na sayar da gidana na hada kudin na yi noma, amma ambaliya ta lalata duk abin da na shuka

Manoma a Jihar Taraba sun tafka gagarumar asara tare da tsintar kansu a mawuyacin hali sakamakon ambaliyar ruwa a 2022, shekara 10 bayan makamanciyar hakan ta faru da su.

Taraba, daya daga cikin jihohin da aka fi noma shinkafa da masara da kuma doya ta tara manoma da ke zuwa takanas daga yankunan Arewa da Yammacin Najeriya domin yin noma.

A kan haka ne muka shiga yankunan jihar, bayan mun yi ta bi ta kauyuka da rugage masu wuyar zuwa, saboda matsalar tsaro da rashin kyan hanya.

A ziyarar tamu, mun ga garuruwa da kauyuka da ruwa ya shanye su gaba daya, sai da muka hau kwalekwale kafin muka tsallaka.

Na yi asarar shinkafa buhu 700 —Manomi

A yankin Ardo Kolla, inda ambaliyar ta shanye gonaki gaba daya, mun yi kicibus da wani manomi mai suna Julde Atiku mai shekara 74, wanda ambaliyar ta shanye gonarsa ta lalata duk abin da aka shuka.

A zantawarmu da dattijon, ya bayyana yadda ruwa ya mamaye katafariyar gonarsa ta shinkata.

“Ruwa ya zo ya mamaye [gonar] gaba daya, har yanzu ruwa ne a ciki, ban isa in je wajen ba sai da jirgi.

“Na watsa akalla iri buhu 10 na shinkafa,” kuma yana tsammanin samun akalla buhu 700 idan ya girbe, amma sai ga ibtila’in ambaliyar.

Ya ce, “Ruwan (Kogin) Binuwai ne ya zo ya mamaye wajen, sannan na [Madatsar Ruwa ta] Lagdo [da ke kasar Kamaru] ya kara [yawan ruwan] ya rufe wajen gaba daya.

“Akalla idan na shiga jirgi daga kauye zuwa gonata, ina yin awa uku, kafin in je wajen.”

Girman asarar da aka yi

Ambaliyar ta yi ajalin mutane da dama tare da lalata gidaje da dukiyoyi, sannan ta mayar da mutane ’yan gudun hijira.

Yawancin manoman yankin sun karbi rance ne suka yi shuka da fatan za su samu amfani mai yawa.

Atiku Julde, ya ce, “Na karbi bashi ne a banki na Naira miliyan 1.5, na zo na fara aikin gonar.

“Sai na ga kudin ba zai ishe ni ba, sai na sayar da gidana miliyan N2.5 na hada na yi aikin gonar.

“Ni a tsammanina na kashe kudi zan samu alheri — abin da nake tsammani shi ne akalla zan samu buhu 700 [na shinkafa],” amma ambaliya ta zo ta lalata komai.

Na koma masunci karfi da yaji —Manomin fadama

Sanin mawuyacin hali da girmar asarar da manoman suka yi sai su ko wanda ya gani.

Barnar da ambaliyar ta yi wa Adamu Bello, wani babban manomin fadama, wanda ta shanye gonarsa baki daya, ta sa dole ya koma yin su domin neman abin da zai ciyar da iyalinsa.

Da muka je inda gonar take, ya ce, filayen wurin “gaba daya gonaki ne, babu irin noman da ba a yi a wannan fadamar.

“Ana noma karamar shinkafa, ana babbar shinkafa, akwai waken suya; Babu irin wadda ba a nomawa.

“Amma da ikon Allah yanzu wurin ya koma fili, babu komai sai ruwa, wani ma bai iya zuwa ya ga gonarsa ba har yau.

“Daga kan tudu ko’ina ka duba ruwa za ka gani, babu halin zuwa gona.”

Ambaliya ta tafi da gidaje —Adamu Bello

Ya ce ambaliyar ta tafi da gidaje da dama a yankin, wanda akasarin mazauna nomama ne.

Wani takwaransa, Adamu Inuwa, ya ce, irin haka ta faru a garin Mudaguli, “Ruwa ya tafi da gidaje gaba daya, [yanzu] mutane sun yi rumfuna suna zaune.

“Sai abin da muka kalata a samu a tura musu.”

Adamu Bello ya ce, “Ni mai magana, idan ka je gonata, ba za ka iya taka kafarka ba.

“Buhu takwas [na iri] na watsa, amma ko kwano daya ban tsira da shi ba.”

Ya ce akwai kananan manoma da asarar da suka yi na abin da suke sa ran girbewa ya kai buhu 100 ko kasa da haka.

Asarar dubban buhunan shinkafa a Tao

Kogin Binuwai ya ratsa ta garin Tao na Karamar Hukumar Ardo Kolla.

Garin ya tara dubban manoman shinkafa daga wurare daban-daban kuma yana daga cikin manyan yankunan da aka fi noman shinkafa a Jihar Taraba.

Amma ambaliyar da aka yi ta jefa yankin cikin rashin tabbas game da makomar noma.

Adamu Inuwa, wani manomi a Tao, ya ce, “Cikin garin Tao kadai an yi asara ta miliyoyin Nairori ta shinkafa zuwa masara.

“Akwai wanda ya watsa shinkafa buhu 30, amma ruwa ya tafi da shi.

“Kamar ni karamin alhaki buhu 20 na iri na watsa, amma ruwa ya dauke; akwai wadanda suka shuka buhu 40, buhu 50, amma duk ruwa ya dauke.

“Duk buhu daya idan an watsa shi, akan samu buhu 100 zuwa 90, idan an fadi ne ake samun buhu 70.”

Na yi noma da rancen N8m, ambaliya ta tafi da komai

Shi ma wani manomi, Muhammad Haruna, wanda ya karbi rance na Naira miliyan takwas domin yin noma na daga cikin wadanda ambaliya ta shanye gonarsu.

Ya ce, “Na karbi rance ya kai na Naira miliyan takwas, amma wannan abin ya zo ya faru, kuma ba mu taba karbar rance ba mu biya ba.”

Muhammad ya ce manoma da dama sun karbi rancen noma, “Tunda dama mun saba karba, muna yi, muna mayarwa; Akwai kungiyoyi daban-daban da ke ba mu rance.”

Ya ce bayan abin da ya faru, suna laluben yadda za su biya bashin da suka karba duk da cewa ruwa ya tafi da abin da duk suka shuka.

‘Ba mu taba ganin irin ambaliyar ba’

Ya ce, “Lokacin da ruwa ya zo abin da muka noma bai isa girbi ba.

“Ruwan ya yi karfi wanda mu kanmu ba za mu iya cire amfanin gonar ba – ga jiragen amma ba halin mu cire.

“A jirgin ma mutum yana tsoron yadda zai hau kan ruwan, tun da ba mu taba ganin ruwa ya zo da yawa haka ba.”

Ya ce sun dauki abin da ya same su a matsayin jarabawa daga Allah.

Barazana ga tattalin arziki

Asarar da manoman suka yi, na barazana ga harkar noma da kuma cigaban tattalin arziki a yankin Kogin Binuwai.

Basaraken yankin Mutum Biyu a Jihar Taraba, Sani Suleiman, ya ce, akasarin mutanen yankinsa sun dogara ne da sana’ar noma, wanda daga abin da suka noma suke cin wani bangare.

“Sannan su sayar da wani bangare su yi amfani da kudin wajen biyan kudin makaranta, yin fufafi, biyan kudin asibiti da sauran bukatu.”

Ya ce yanzu abin da ya same su, “Na barazana gare mu da ma kasa baki daya.

“Shinkafar da ake nomawa a nan ce ake kaiwa sassan kasar nan har a fitar kasashen waje.

“Daga Mutum Biyu, Gassol, ana daukar shinkafa a kai jihohin Nasarawa, Jigawa, Borno, Sakkwato da Kebbi.

“Akwai manyan manoma daga Kebbi da ke zuwa nan su yi noman damina.

“Na san wai manomi da ya shuka buhu 100 na iri a gonarsa, amma da amabliyar ta zo bai tsira da komai ba.”

Musabbabin matsalar

Masana sun danganta matsalar ambaliyar ga sauyin yanayi da kuma ayyukan dan Adam da ke gurbata muhalli.

Hakan, a cewarsu, ya yi gagarumar illa ga harkar noma wadda mutane da yawa suka fi dogaro da ita — wadda kuma ke ciyar da kasa — a Najeriya da makwabtanta, Kamaru, Nijar da Chadi.

Wani abin da ke haddasa ambaliya kuma shi ne rashin daukar matakan da suka dace wajen hana aukuwar ambaliyar.

Dokta Vincent Ojeh, Masanin Yanayi a Jami’ar Jihar Taraba, ya ce, “Ana iya danganta sashen matsalar da ayyukan dan Adam a birane.

“Sannan babban abin da ke kawo ambaliya shi ne tasirin sauyin yanayi.

“Akwai rashin tabbas game da yanayin ruwan sama; Misali, ko da Hukumar Binciken Yanayi ta Kasa (NiMET) ta yi hasashe, da kyar a iya sanin yawan ruwan – sai da wadatattun kayan aiki.

“To duk lokacin da aka yi mamakon ruwa, wanda kasa ba za ta iya shanyewa ba, akwai yiwuwar samun ambaliya.

“Wanna shi ne abin da muke shaidawa a Najeriya.”

Bashi ya yi wa manoma katutu

Tun shekarar 2015 da Gwamnantin Shugaba Buhari ta haramta shigo da shinkafar waje, yawancin ’yan Najeriya suka koma cin ’yar gida.

Sai dai yanzu yawan ambaliya da asarar da take haddasawa ta sa bashi ya yi wa yawancin manoma katutu.

“Ambaliyar ta kawo matsala ga manufar hadin gwiwar da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi da Kungiyar Manoman Shinkafa ta Najeriya (RIFAN) na wadatar da kasa da shinkafa da kuma ganin kasar ta dogara da shinkafar da ake nomawa a cikin gida.

“Sai da muka cimma kusan kashi 70 cikin 100 a kokarin ganin an samu daidaito da wadatuwar shinkafar gida a Najeriya, ta yadda ba za mu bukace ta daga wani wuri ba.

“Amma yanzu ambaliya ta mayar da hannun agogo baya” in ji Tanko Bobboi, shugaban RIFAN, Reshen Jihar Taraba.

Mene ne abin yi?

Ya ce, “Dole sai CBN da RIFAN da kuma Gwamnatin Tarayya sun sake shiri domin farfado da shirin da kuma cike gibin da za a samu a bangaren noman shinkafa.

“Idan ko ba haka ba, to kamar yadda aka fara ganin alamu, za a iya fadawa cikin matsalar yunwa.

“Domin idan har magidanta a Taraba na fargabar rasa shinkafa, to ina ga wadanda suka dogara da shinkafar da ake kai musu daga nan a jihohin Kano, Gombe, da sauransu?

“Saboda haka akwai barazanar samun karancin abinci a sakamakon wannan ambaliyar.”

Manoman masara na neman tallafi

Shugaban Kungiyar Masara ta Najeriya Reshen Jihar Taraba, Yusuf Mijinyawa, ya roki Gwamnatin Tarayya ta yi musu tallafi da taimako, “Ta hanayar sake ba su kayan aiki” saboda abin da ya same su.

Ya bayyana cewa abin da manoma suka yi amfani da shi wajen noman da suka yi asara rancen banki ne da suka samu a matsayin kungiyarsu daga Bankin CBN.

“To ka ga wannan bashi yana nan a kan manoma ko a kan kungiyar.

“Idan gwamnati ta shiga ciki ta tallafa da kayan aiki, inda za a sake aikin ko da na rani ne, …to zai iya taimakawa wajen ganin cewa an samu abincin.

“Amma idan ba haka (aka yi ba) to akwai matsalar abinci a Jihar Taraba da ma Najeriya, sakamakon wannan ambaliyar.”

Matakin da ya kamata

Dokta Vincent ya bayyana cewa, duk da cewa ayyukan dan Adam sun taka muhimmiyar rawa wajen aukuwar ambaliya a 2012 da kuma 2022, gwamnati ta fi kowane bangare girman alhaki wajen shawo kan matsalar.

“Abu na farko shi ne daukar matakan hana aukuwar hakan, wanda ya kunshi gina madasun ruwa da kuma dakatar da gurbacewar iska da ke haddasa sauyin yanayi,” in ji shi.

Daya hanyar kuma a cewarsa, it ace daukar matakan rayuwa a yanayi ko wuraren da ake samun ambaliya da suka hada da sauya muhalli daga wuraren ruwa ke mamayewa da sauransu.

Ya bayyana cewa wannan na bukatar taimakon gwamnati da kuma kungiyoyin jinkai, saboda a wasu wuraren gaba daya garin ne ruwa yake mamayewa a lokacin ambaliya.

“Za a iya hasashen wuraren da za a samu ambaliya, amma abu mai wuya ne a ayyana hakikanin lokacin.

“Amma idan aka dauki matakan kariya, ko aka tashi daga wurin, akalla za a tsira da wani abu ko a rage girman asarar,” kamar yadda masanin yanayin ya bayyana.

Barnar da ambaliyar 2022 ta yi a Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta ce kawo yanzu, ambaliyar 2022 ta shafi rayuwar mutum miliyan 3.2, a yayin da miliyan 1.4 suka rasa muhallansu a kasar.

Iftila’in ya kuma yi ajalin mutum 612, inda Jihar Jigawa ce kan gaba da yawan mutum 91, a yayin da a Jihar Kogi ta shafi rayuwar 471,991.

Wannan yanayi na neman ya gagari kundila a wajen hukumomin ba da agajin gaggawa na jihohi da ma tarayya.

Aikin agajin gaggawa

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta bayyana irin kokarin da take yi kan matsalar da aka samu a bana.

Shugaban Sashen Ayyuka na Ofishin NEMA na Adamawa/Taraba, Ladan Ayuba, ya ce baya ga asarar dukiyoyi da muhallai, ambaliyar bana ta yi ajalin mutum 40 a Jihar Adamawa, da kuma 37 a Taraba.

“Muna kwashe mutane daga wuraren da aka yi ambaliya zuwa kan tudu.

“Saukinta dai shi ne mutane na nuna karamci wajen saukar da baki a gidajensu.

“Kofarsu a bude take su saukar da ’yan uwa da dangi da abokan arziki a gidajensu.

“Shi ya sa ba a ganin yaduwar sansanonin masu gudun hijira a yankin.

“Idan kuka lura za ku ga babu sansanin ’yan gudun hijira, saboda mutanen sun samu wadanda suka ba su masauki,” in ji jami’in.

Game da asarar da manoma suka yi, ya bayyana cewa, “Mun zagaya yankunan da abin ya faru, mun gani da idonmu, mun tura rahoto, domin gwamnati ta bayar da kayan tallafi.”

Sai dai kuma wani abin da ake kuka da shi shi ne, ba lallai ne tallafin da gwamnati ta fitar ya kai ga ainihin manoman da suka dace ba.