Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin zai yi nazari kan bukatar da ya kira mai girman gaske ta neman sakin Nnamdi Kanu, shugaban masu fafutikar kafa kasar Biyafara.
Wannan alwashi na zuwa ne yayin da kungiyar dattawan al’ummar Ibo suka gabatar masa ne neman sakin Kanu.
Kawo yanzu dai Kanu wanda ake zargi da aikata ta’addanci a gaban kotu, na hannun ’yan sandan farin kaya na DSS sakamakon gwagwarmayar da yake yi ta neman kafa kasar Biyafara a kudancin Najeriya karkashin kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) da aka haramta.
Buhari ya bayyana hakan ne yayin da yake karbar bakuncin manyan masu fada a ji na al’ummar Ibo a fadarsa da ke Abuja ranar Juma’a karkashin jagorancin tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Mbazulike Amaechi.
“Bukatar da kuma nema a wurina na da matukar girma a matsayina na shugaban wannan kasa. Tasirin bukatar taku na da girma sosai,” a cewar Buhari cikin wata sanarwa da Femi Adesina ya fitar.
Ya kara da cewa bukatar da dattijan suka nema “ta saba wa tanadin tsarin mulki da ya fayyace tsarin shugabanci tsakanin gwamnati da bangaren shari’a.
“Cikin tsawon shekara shida da na shafe a matsayina na Shugaban Kasa, babu wanda zai iya cewa akwai wani lokaci da wajen gudanar da aiki na yi wa bangaren shari’a katsalandan kan abin da huruminsu ne.
“Sai dai bukatar da kuka gabatar mai girma ce sosai amma zan yi nazari a kanta,” in ji shi.
Sanarwar ta ce Shugaba Buhari ya kuma jajanta wa tsohon Ministan, Mista Amaechi, wanda a bayan nan ya binne gawar matarsa da ta riga mu gidan gaskiya, inda ya yi mata addu’ar da fatan mutuwa ta zamto hutu a gare ta.