✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na yi abin da ya dace kan cire tallafin man fetur — Tinubu

Bai kamata Najeriya ta ke azurta wasu mutane kalilan da kudin tallafin man fetur ba.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kare matakin da ya dauka na cire tallafin man fetur, inda ya ce ya yi abin da ya dace.

Daraktan yada labarai na Fadar Shugaban Kasa, Abiodun Oladunjoye, ya ruwaito shugaban kasar ya bayyana haka a ranar Juma’a a wani taro da ya yi da sarakunan gargajiya.

Ya kuma bayyana tallafin a matsayin abin da ke durkusar da kasar nan domin tana fama da matsalar biyan albashi.

Shugaban ya ce bai kamata Najeriya ta zama kan gaba na kasashen da ke biyan tallafin man fetur.

“Na gode da kuka mai da hankali ga abin da nake yi. Kun kula da cire tallafin. Me ya sa ya kamata mu kasance cikin wannan yanayi, muna azurta wasu mutane kalilan.

“Abin da zai durkusar da Najeriya shi ce tallafin man fetur. kasar da ba za ta iya biyan albashi ba kuma sai mu dage da biyan tallafi. Ina ganin mun yi abin da ya dace.”

Shugaban ya kara da cewa gwamnatinsa za ta saurari shawarwari daga kowane bangare.

“A shirye muke mu saurari shawarwari a kowane lokaci. Na yi muku alkawarin bude kofata a ko da yaushe a gare ku,” in ji shi.

Aminiya ta ruwaito cewa, a jawabinsa na farko bayan rantsar da shi a matsayin Shugaban Najeriya a ranar 29 ga watan Mayu, Tinubu ya sanar da cewa wa’adin biyan tallafin man fetur a kasar ya kare