Zababben Shugaban Kasa, Bola Tinubu ya ce ya shirya sauke nauyin al’ummar Najeriya da zai rataya a wuyansa da zarar ya sha rantsuwar kama aiki.
Tinubu ya bayyana haka ne jim kadan bayan ya dawo kasar bayan shafe kusan wata guda a birnin Paris na kasar Faransa.
Tinubu ya ce ya yi farin cikin dawowa Najeriya bayan hutun mako biyar da ya yi a birnin Paris na kasar Faransa.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa Tuwita, Bola Tinubu ya ce ya yi matukar farin ciki da annashuwa kan irin gagarumar tarbar da aka yi masa a lokacin da ya sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
Zababben shugaban ya kuma gode wa dimbin masoya da magoya bayansa kan irin kaunar da ya ce suna nuna masa.
Ya kara da cewa yana nan a kan alkawarin da ya dauka na samar da sabuwar Najeriya.
Tinubu ya kuma ce yana cikin koshin lafiya sabanin jita-jitar da ake yadawa cewa yana fama da rashin lafiya.