✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na shiga sana’ar fasa dutse don biyan kudin makaranta -Haladu Barawa

Sana’ar fashin dutse ta karfi ce, wadda ba ta dade da shigowa Arewa ba. Sana’ar tana cike da hadarin samun raunuka, imma dai lokacin da…

Haladu Hamza Barawa ke nanSana’ar fashin dutse ta karfi ce, wadda ba ta dade da shigowa Arewa ba. Sana’ar tana cike da hadarin samun raunuka, imma dai lokacin da ake fasa dutsen da hannu ko sanya nakiyar fasa shi, kafin a mayar da  shi kanana daban-daban gwargwadon yadda masu saye ke bukata. Haka nan sana’a ce da ba kowa ne ke iya yin ta ba, saboda yadda take. Haladu Hamza Barawa, matashi ne mai himma, dan shekara goma sha biyar, wanda ya dauki gabarin nema wa kansa abin yi don dauke wa mahaifansa nauyin biyan kudin makaranta. Aminiya ta yi kicibis da shi a garin Barawa, daya daga cikin wuraren da ake gudanar da wannan sana’a ta fashin dutse a Jihar Katsina, inda ta zanta da shi, kamar haka:
Aminiya: Ka yi makaranta, kuma me ya sa ka shiga sana’ar fasa dutse?
Haladu: E, ina cikin karatun ma a yanzu haka, a makarantar sakandare ta jeka-ka-dawo da ke Bakiyawa. Na shiga wannan sana’a ne saboda in rika biyan kudin karatuna, saboda iyayena talakawa ne, ba za su iya daukar nauyina ba. To maimakon in yi maula ko bara, ya sa nake yin wannan sana’a, kuma yanzu na kai shekara biyu ina yi, har ta kai ma na saba, ba na jin komai a jikina.
Aminiya: Kudin makarantar ne kawai kake biya ko akwai wani abin daban?
Haladu: Da kudin makarantar da kuma wadanda zan dan rika kashewa, kuma ina tallafa wa iyayena da wani abu.
Aminiya: Akwai wani kebantaccen wurin gudanar da sana’ar ne ko duk inda mutum ya ga ya yi masa yake yi?
Haladu: E, akwai wurin da muke zuwa inda muka san za mu samu aikin, kamar yadda nake yi a nan.
Aminiya: Shin awo ake saye ko tarin wabda aka fasa?
Haladu: Kamar mutum in ya buga ya tara, ana zowa ne a auna a biya shi, kowane baro Naira dari. Nakan yi nawa aikin ne idan na taso daga makaranta.
Aminiya: Ko wannan sana’a na da hadari?
Haladu: kwarai kuwa domin lokacin da kake bugun dutsen, zai iya bulla ya bugar maka kafa ka ji rauni, ko lokacin da aka sa nakiyar fasa tsaunin ko gundarin dutse, in an samu akasi, sai wani tsautsayi ya auku.
Aminiya: Duk da haka, yaya kake kallon sana’ar?
Haladu: Gaskiya sana’a ce ta rufin asiri. Ka ga baya ga hidimar makaranta da ta iyaye, har akuya da tunkiya na saya da sana’ar. Kuma, in har na bar wannan sana’a, to kudi na samu manya, kuma alhamdulillahi, babu ruwana da wata shegantaka ta abokai a kan wannan.
Aminiya: Ko mene ne kayan aikin ita wannan sana’a?
Haladu: To mu masu bugawa, kulki (guduma) shi ne babban kayan aikinta. Ga manyanmu kuma nakiyar da suke sawa; sai shebur da kuma baro na awo.
Aminiya: Wane kira za ka yi, musamman ga matasa?
Haladu: Kiran shi ne matasa su rungumi sana’ar da za su rufa wa kansu asiri, maimakon yin maula ko amfani da su wajen aikata ayyukan assha. Kuma kada su raina duk irin sana’ar da ta shigo hannunsu domin ta fi zaman kashe wando.