Sauyin zamani ya kawo canji a sana’ar kitso kamar yadda makitsiya Maryam Idris ta shaida wa Aminiya a Kalaba.
Makitsiyar ta ce ta shafe shekara sama da 30 tana yin sana’ar kitso a garin Kalaba Jihar Kuros Riba.
- ’Yan bindiga sun yi awon gaba da matar dan sandan kwantar da tarzoma wasu mutum 5 a Zariya
- COVID-19 ta kama sama da mutum 100,000 a Faransa ranar Kirsimeti
Ta cewa saboda ta samu abin da za ta rufa wa kanta asiri ne ta fara wannan sana’a ta yin kitso, kuma babu abin da zata ce domin ta samu rufin asiri a cikinta.
Ta ci gaba da cewa sauyawar zamani ya sa an bar irin kitso na da can da ake yi, wanda a yanzu akwai nau’in kitso kala dabam-dabam, amma kuma duk da hakan ina yin duk irin wanda ya samu.
“A can shekarun baya akwai nau’in Kitso kamar Iko ta Tuntsiro, Kalaba, Shukku duk da zamani ya sanya yanzu ba’a yi amma idan mace tazo tana da bukata ina yi.
“Sai dai mafi akasarin matan da suke zuwa ina ga dai-dai ne suke yarda a yi musu kitso irin nada din, sai dai na zamani,” inji ta.
A cewarta, yawanci abokan ma’amalarta sun fi son na zamanin nan.
Kazalika ta bayyana kalubalen da ta taba fuskanta tace komai dai Alhamdulillahi amma dai wani lokacin wasu kan zo ka yi musu kitso, bayan kun yi jinga ga abin da za su biya, sai idan ka gama ku fara kace- nace a kan biyan kudin.
Hajiya Maryam ta ce ta yi wani kitso da ta samu alherin da ba za ta taba mantawa ba a rayuwarta.
Ta kara da cewa tana yi wa mata ma’aikata kai har ta taba yi wa matar Gwamna Kitso.
“Na taba yi wa matar Gwamnan Kuros Riba Kitso kuma ta yi min alheri sosai’’ inji ta.