✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na samu rufin asiri a kasuwancin manja – Alhaji Aminu

Wani dan kasuwa da ke sayar da manja da man gyada a babbar kasuwar da ke tsakiyar birnin Bauchi, Alhaji Aminu Mai Manja, ya ce…

Wani dan kasuwa da ke sayar da manja da man gyada a babbar kasuwar da ke tsakiyar birnin Bauchi, Alhaji Aminu Mai Manja, ya ce akwai rufin asiri “kwarai da gaske” a kasuwancin manja da man gyada wanda ya kwashe shekaru yana yi.
Ya ce: “lokacin da na fara kasuwancin manja da man gyada mutane da dama suna mun dariya, amma cikin ikon Allah kasuwancin manja ya yi mun komai a rayuwa ina da rufin asiri daidai bakin gwargwado.”
dan kasuwan ya kuma ce akwai wasu daga cikin yara da yake koya musu yadda ake kasuwancin. Ya ce “ina goyon bayan a koya wa mutum yadda ake kama kifi, ya fi a ba mutum kifin. Allah ne kadai zai iya ba ka kullum ba tare da gajiyawa ba.”
“Ina ba da shawari ga gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi har da shugabannin kananan hukumomi da su dage sosai wajen wayar da kan matasa ta kafafen watsa labarai game da illolin da ke tattare da yawon roko a tsakanin al’umma,” inji shi.
Ya ci gaba da cewa: “A matsayina na matashin dan kasuwa, ina ganin idan gwamnati ta bunkasa aikin noma da kiwo da taimaka wa kananan ’yan kasuwa wadanda ba su da jari mai yawa, tattalin arzikin kasar nan zai bunkasa domin akwai alheri sosai a kasuwanci, amma sai mutum ya yi hakuri domin ba a fafe gora ranar tafiya.”
“Ina fatan bayan an shiga kasuwanci a hada da neman ilimin addini da na zamani domin yanzu duniya ta sauya ana tunkaho da ilimi ne ba da yawon sa sabbin ruguna ba. Don haka ina kira da babbar murya ga matasa da su yi watsi da zaman kashe wando domin babu al’ummar da za ta samu ci gaba mai amfani sai matasanta sun kasance masu dogaro da kansu.”