✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Na rabu da mai neman aurena kan raina Kwankwaso —Budurwa

Budurwar ta ce a kan Kwakwaso, za ta iya rasa ranta.

Wata budurwa a Kano ta lashi takobin watsi da duk saurayi da zai nemi auren ta matukar yana nuna rashin ladabi ga tsohon Gwamnan Jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Budurwar wadda ta ce sunanta Lubna Ali, ta ce, a kan Kwakwaso za ta iya rasa ranta, kuma da ta auri wanda ba ya martaba shi, gara ta zauna har ababa ba ta yi aure ba.

“Na yi watsi da baikon wani manemin aurena saboda Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, duk da cewa Kwankwason ko sani na bai yi ba, amma a kansa zan iya karbar harsashi,” inji ta.

Ta ce, “Ba a matsayin dan siyasa kawai nake kallon Kwankwaso ba, a’a ina kallon sa ne a matsayin jagora, uba kuma abun koyi.”

A cewarta, tun tana aji daya na Karamar Sakandire a shekarar 2003 take tsananin kaunar salon Kwankwason na tafiyar da lamuransa.

“Tun ban ma san me Siyasa ke nufi ba, na haddace sunan Kwankwaso.

“Ba zan manta ba,  motar da na fara mallaka ja ce kirar 406 kuma jikinta ko’in a like yake da hotunan Kwankwaso,” inji ta.