✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na koyi sana’o’i da yawa don gudun zaman banza -Sinan Tela

Wani matashi mai suna Sinan Tamim Aliyu, dan kimanin shekaru 29, da ke sana’ar gyaran keken dinki a Legas ya ce ya koyi sana’o’i da…

Sinan Tela lokacin da yake gyaran wani keken dinki.  Wani matashi mai suna Sinan Tamim Aliyu, dan kimanin shekaru 29, da ke sana’ar gyaran keken dinki a Legas ya ce ya koyi sana’o’i da dama domin ya yi maganin zaman banza.
Sinan Tamim, dan asalin garin Jos da ke Jihar Filato, wanda ake yi masa lakabi da Sinan Tela ko kuma Akto, ya shaida wa Aminiya cewa ya iya sana’o’i da yawa, wadanda suka hada da sana’ar gyaran keken dinki da dinkin kayan sawa da na kayan sanyi na yara da kuma gyaran wuta.
Ya ce, “Ka san yadda zamani ya canja yanzu, idan ba ka iya sana’a ba, kana iya shiga wani hali. Saboda haka ne na koyi sana’o’i da yawa, don idan daya ta tsaya, sai na ci gaba da wata. Misali idan dinki ya tsaya, sai na koma gyaran keken dinki, ko gyaran wuta. Ka ga babu yadda za a yi na zauna haka ba tare da ina samun dari da kwabo ba”.
Ya ce, “Ba wanda ya koya mini gyaran keke, karambanina ne kuma Allah Ya taimake ni na iya har na kware, shi ya sa wani lokaci kyauta nake yi wa jama’a aiki. Wani lokaci ma har boye wadansu sana’o’in da na iya nake yi saboda kada mutane su dame ni”.
Sinan, mai matar aure daya da ’ya’ya biyu ya bayyana cewa ya samu nasarori da yawa tare da rufin asiri a rayuwarsa, sai dai kalubalen da yake fuskanta shi ne na rashin hakuri daga masu kawo masa gyara. “Idan mutum ya kawo maka gyara, sai ya rika azalzalarka, yana so ka yi gaggawa, sakamakon haka wani lokaci wajen sauri, sai ka lalata wani abu a jikin kayan da aka kawo maka kuma sai ka biya. Shi ya sa wani lokaci nake yin gyaran kyauta, yadda mutum ba zai takura mini ba”. Inji shi
Ya ce hada sana’o’i da yawa a lokaci guda yana da wuya saboda kalubalen da ke tattare da rayuwa a zamanin da muke ciki. “Domin zai kasance kana cikin yin wata, sai wani ya zo ya ce yana so ka yi masa wani aiki. Ka ga dole wani lokaci ka bar sana’ar da kake yi a lokacin ka tafi ka je ka yi wacce kake ganin za ta kawo maka kudi”.
karshe ya yi kira ga matasa su rungumi sana’a su guji zaman banza don ba abin da yake haifarwa sai mutuwar zuciya, wacce ke kai mutum ga halaka.