✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na ki ba Shata kudi kan wakar da ya yi min – Sani Zangon Daura

Alhaji Sani Zangon Daura na daya daga cikin mutane da Alhaji Mamman Shata, ya yi wa waka, saboda kauna, kuma ya ce, ya ki ba…

Alhaji Sani Zangon Daura na daya daga cikin mutane da Alhaji Mamman Shata, ya yi wa waka, saboda kauna, kuma ya ce, ya ki ba Shata kudin wannan waka da ya yi masa:

Amshi: Alhaji Sani Zangon Daura
Sa’in nan yana dan yaro, yana karami nai in na lallabo zan karba
Alhaji Sani Zangon Daura
Sai ya ce ina karamina, ina makaranta, sai ya ce ni almajiri mabaraci
Alhaji Sani Zangon Daura
Tunda ka girma ka zama Malam, bari in lallabo in karba,
Alhaji Sani Zangon Daura
Ba mu rabonmu na Mamman Daura
Alhaji Sani Zangon Daura

Mene takaitaccen tarihin dattijo?
Sunana Alhaji Sani Zangon Daura, an haife ranar 31 ga watan Disamba 1938 a garin Zangon Daura da ke Jihar Katsina, a yanzu ina da shekara 77.
Na yi karatun allo sannan na fara na boko a makarantar firamare ta Zango, sannan na wuce Makaratar Midil ta Katsina inda na kammala sannan na wuce Makarantar Koyon Harshen Larabci ta Kano (SAS) inda na samu shaidar zama Malami Mai daraja ta Biyu. Na fara koyarwa a Makarantar Firamare ta Zangon Daura sannan na samu karin girma zuwa Babbar Firamare ta Daura. Daga nan aka mai da ni Hukumar Lardi ta Katsina inda aka tura ni Babbar Firamare ta Dutsinma.
Yaya aka yi ka ci gaba da karatu?
Na samu tallafi daga hukumar tallafin karo ilimi ta Jihar Arewa don karo karatu a kasar Sudan a fannin ilimin addinin Musulunci bayan na ci jarrabawar GCE. Sai na ruga Kano don lokacin marigayi Ministan Ilimi Alhaji Isa Kaita yana rangadi a Kano, na ce ina son in je in yi karatu ne a Ingila. Bayan makonni biyu na samu dama zuwa Makarantar Koyon Larabci ta Landan. Na yi karatun share fagen shiga jami’a a Ingila, bayan na kammala aka ba ni damar fara karatun digiri.
Me ya sa ka bar Landan ka dawo Najeriya don ka kamala karatu?
Ba zan fadi.
Amma abokanka sun bar Ingila don yanayin sanyin garin ya dame su?
Sanyi na daya daga cikin ababen. Abin mamaki shi ne yadda ma’aikata na da suka sha bamban da na yanzu, shi ne dagewa kan ciyar da kasa gaba. Don shugaban hukumar bada tallafin karatu Alhaji Muhammad Daku ya yi ta tuntubar jami’o’i don su ba ni dama. Jami’ar Ahmadu Bello ta ba ni fannin shari’ar Turawa, amma na ki don na fi son karanta harkar tsimi da tanadi. Sai na niki gari na nufi Ikko na je na yi karatun digiri a fannin harkar kasuwanci a Jami’ar Legas.
Kana jin harshen Yarbanci?
(Dariya), Yarbawa ba sa sonmu, don haka na ki koyon yaren, sai dai na san kalma daya ‘Munbo’ wato ina zuwa. Amma ba zan fadi dalilin da ya sa na san hakan ba.
Yaya ake daukar aiki a lokacin?
Za a tantance ku sannan a ba ku takardar daukar aiki, ana neman ma’aikata a lokacin. Na fara aiki a matsayin jami’i mai daraja ta biyar aka tura ni Ma’aikatar Ilimi.
Yaya aka yi ka yi aiki a IIori?
Jihar Arewa ta dauke ni aiki, kuma Ilori na karkashinta, wannan ya sa bayan na yi wata uku a Kaduna sai aka tura ni Lardin Ilori. Bayan na isa, sai aka tura ni yankin tsohowar Bussa, wacce ake ce wa Kainji a yanzu a matsayin mataimakin jami’in lardi. Ina nan ina aiki sai Gwamnan Arewa ta Tsakiya Birgediya Abba Kyari ya nada ni Kwamishinan Yada Labaru da Wayar da kan Jama’a da Aikin Gayya. Bayan shekara uku zuwa hudu aka mayar da fannin cikakkiyar Ma’aikatar Yada Labaru a 1972. Daga nan sai aka mayar da ni Ma’aikatar Lafiya da Jin Dadin Jama’a. Bugu da kari, bayan Janar Murtala Muhammad ya yi wa Janar Yakubu Gowon juyin mulki, sai aka ba mu damar ko za mu ci gaba da aiki, sai na ce ni zan yi murabus in huta don zan koma harkar kasuwanci.
Wane harka ka dauka a fannin kasuwancin?
Daga 1973 zuwa 1993, na shiga harkar kwangila da masana’antu da zama darakta a kamfanoni kimanin goma sha biyar da kuma harkar noma da kiwo gadan-gadan.
Mene ne dalilin da ake cewa kana da sa’a a harkokinka?
daya daga ciki shi ne lokacin da na shiga siyasa inda na yi takarar Gwamnan Tsohuwar Jihar Kaduna da ta kunshi tsofaffin Lardunan Katsina da Zazzau a 1983 a karkashin Jam’iyyar NPN lokacin mulkin Shugaba Shehu Shagari. Amma Allah bai sa na yi nasara ba a zaben fidda-gwani na jam’iyyar, Alhaji Lawal Kaita ya yi nasara. Amma bayan wata uku sai sojoji suka yi juyin mulki. Sannan aka kama masu rike da mukaman siyasa aka garkame su a gidan maza. To ka ga ai ni Allah Ya yi min gyadar-dogo don ni ba a kama ni an tura a kurkuku ba.
Yaya aka yi ka halarci tarurrukan tsara kundin mulkin kasa daban-daban?
A 1977 zuwa 1978 na halarci wanda Janar Obasanjo ya shirya lokacin ya gaji shirin marigayi Janar Murtala Muhammad. A lokacin muka shirya kundin tsarin mulki na 1979 wanda ake yi wa lakabi da ‘Kundin mutum 49 masu basira.’ Sannan na biyu shi ne wanda Janar Sani Abacha ya shirya tsakanin 1994 zuwa 1995.
Mene ne dalilin da ya sa ka jingine aikin Minista a lokacin mulkin Obasanjo na farar hula?
A 1999 aka maido da mulki hannun farar hula inda Obasanjo ya nada ni a matsayin Ministan Aikin Gona sannin ya tsige ne don karfin mulki irin nasa.
Mene dalilin da ya sa ya cire ka?
Ya fi daidai in ka ce ya tsige ni, ko ya tumbuke ni daga mukamin Minista. Amma ba zan fada ba a yanzu don wata ran zan rubuta kammalallen tarihina da bayanin abin da ya faru tsakanina da mai tsananin mulki irin na Obasanjo.
Mene ne dangantakarka Sani Zangon Daura da Malam Mamman Daura and Janar Muhammadu Buhari?
Malam Mamman Daura ajin mu daya a makaranta. Janar Muhammadu Buhari na bayanmu a makaranta. Malam Mamman Daura kawun Buhari ne don shi kani yake ga mahaifin Buhari. Ni kuma garinmu ne daya. Kuma dukansu na dauke su a matsayin abokai, ’yan uwa kuma shakikai.
Yaya aka yi kake abota da Janarori Buhari da Babangida da Aliyu Gusau?
Ba na munafunci. Ban daukar maganar daya in kai wa daya. Amma ba ta hana in gaya wa mutum gaskiyar ra’ayina ba.
Yaya aka yi Mamman Shata ya yi maka waka lokacin kana makaranta, bayan masu kudi na ta gogoriyon ya yi musu amma ya ki?
Lokacin in na zo hutun makaranta ina zuwa wurin Minista Mamman Bashar wanda daga bisani ya zama Sarkin Daura kafin Allah Ya yi masa rasuwa. To a matsayinsa na ubangidan Shata, bayan da Shata ya yi masa wakoki sai ya yi min. Ya kuma lallabo yana neman kyauta, sai na ce masa ina makaranta. To ashe yana nan bai manta ba. Bayan an jima na fara aikin koyarwa sai ya zo neman samu, ni kuma na ce masa ai ni Malami ne mai lallaba albashinsa.
Bayan ka zama babban ma’aikaci a ofishin Gwamna Birgediya Abba Kyarai a Kaduna ya zo neman ladar wakar?
Ya zo, amma ni ban ba shi kudi don ya yi min waka kamar yadda ya yi wa ubangidana Minista kuma Sarkin Daura Mamman Bashar ba. Don lokacin muna aikin gwamnati, aiki kawai ake yi tsakani da Allah ba almundahana a lokacin. Sai na gaya masa ai ni ma’aikaci ne.
A takaice ka biya kudin wakar da ya yi maka?
A’a ni ban ba shi kudi ba. Domin ni ban sa shi ya yi min waka ba. kauna ta sa ya yi min waka.
Yaya mu’amamalarku take da shi zuwa rasuwarsa?
Alaka ce mai karfi don ni da shi muna da ubangida guda. Kuma in mun hadu muna girmama juna matuka har Allah Ya yi masa rasuwa.