Kwararriyar mai girke-girken nan da ta shiga kundin tarihi na Guinness a matsayin wacce ta fi dadewa tana girki a duniya, ta ce Naira miliyan 80 ta kashe yayin gasar girkin da ta yi a kwanakin baya.
A ranar Talata ce kundin adana bayanai na Guinness World Records ya tabbatar da Hilda a matsayin bayan ya ce ta shafe awa 93 da minti tara tana girki ba kakkautawa.
- Dan ‘jam’iyyar adawa’ ya zama Shugaban Majalisar Dokokin Imo
- A kokarin tserewa, mai garkuwa da mutane ya yanke jiki ya fadi ya mutu
Sai dai jim kadan da sanar da sakamakon, wani kamfani ya zarge ta da karya alkawarin wata yarjejeniya da ya ce ya kulla da ita ta shirya wani taron sada zaumunci kan Naira miliyan uku a Abuja.
To sai dai da take mayar da martani, Hilda ta ce sai da ta kashe miliyan 80 na halaliyarta a girke-girken, kuma ma ta ce ba ta da masaniya a kan waccan yarjejeniyar da kamfanin.
Ta ce, “Na kashe sama da Naira miliyan 80 na kudin da na yi gumi na tara, domin mutane su ci su sha, a kyauta.”
Idan za a iya tunawa, a ranar 11 ga watan Mayu, da misalin karfe 4:00 na yamma ta fara girkin a hukumance, inda ta shafe awa 100.
Sai dai daga baya kundin na Guiness ya ce bayan tantancewa da nazari, ya rage tsawon lokacin zuwa awa 93 da minti 10.