✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan ‘jam’iyyar adawa’ ya zama Shugaban Majalisar Dokokin Imo

LP dai na da kujeru 14, PDP 10 a majalisar

Dan jam’iyyar adawa ta PDP, Uche Ugwu, ya zama Shugaban Majalisar Dokkin Jihar Imo wacce mambobin jam’iyyar LP ke da rinjaye a cikinta.

Uche dai shi ne dan majalisa mai wakiltar mazabar Udi ta Arewa.

Majalisar Jihar dai na da mambobi 24, inda 14 daga ciki ’yan LP ne, yayin da PDP take da mambobi 10.

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Nkanu ta Yamma, Iloabuchi Aniagu, ne ya ba da shawarar nada sho, ragowar ’yan majalisar kuma suka amince da shi.

Kazalika, an kuma zabi dan majalisa daga mazabar Igboetiti ta Yamma, Prince Ezenta Ezeani, a matsayin Mataimakin Shugaban majalisar.

Sai dai kuma an dage zaman majalisar da tare da an rantsar da mambobinta ba, har zuwa ranar Juma’a mai zuwa.

Kodayake ba a bayyana makasudin yin hakan ba, ana hasashen ba zai rasa nasaba da kasancewar Gwamnan Jihar, Hope Uzodinma ya bar Jihar ba, saboda shi ne Shugaban kwamitin zaben Shugaban Majalisar Dattawa na jam’iyyar APC.