✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Na kashe budurwata don in yi tsafin kudi —Matashi

Matashin ya amsa cewa ya kashe budurwasa ne don yin asirin kudi.

Wani matashi mai shekaru 31 a duniya a Jihar Osun ya amsa cewa shi ne ya kashe budurwasa saboda ya yi arziki.

A yayin tattaunawarsa da Aminiya, wanda ake zargin ya amsa cewa shi ne ya datse kanta, don ya yi asirin da zai yi arziki.

Ya ce ‘yan uwanta ba su san ta je gidansa, don kai masa ziyara ba, sai da ake neman ta ne wani ya yi zargin ko ta je gidan nasa.

Bayan batar budurwar, iyayenta sun shigar da kara hedikwatar ‘yan sanda ta Iwo, a shekarar da ta gabata.

Daga baya kuma an mayar da binciken batar nata Sashen Zurfafa Bincike da Fikira da ke Osogbo, a Jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Wale Olokode ya ce an kama matashin ne bayan samun wasu bayanan fikira da jami’ansu suka samu.

Olokode, ya kara da cewa wanda ake zargin ya kashe mutane da dama, sannan ya yi fice wajen sayar da sassan jikin mutane.

Wanda ake zargin, ya ce wayar budurwar tasa da ya kashe shi ne abin da ya tona asirinsa.

Ya sayar da wayarta kan N2,000 bayan da ya kashe ta, jami’an tsaro sun bi diddigin wayar har suka samo wanda ya saya, daga bisani kuma suka cafke shi.

Jami’an ‘yan sanda sun samu gawar budurwar da ta wani da ya kashe a wani rami da ya binne su.

Kwamishinan ‘yan sandan, ya ce suna ci gaba da bincike domin kamo wanda yake hada baki da su wajen aikata wannan mummunar sana’a ta sa.