✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na ji dadi da tafiyar Maguire zuwa West Ham ta samu tangarda — Ten Hag

Sai dai fa dole ne Maguire ya dage domin dawo da martabarsa a kungiyar.

Erik ten Hag ya ce ya yi farin ciki da Harry Maguire ya ci gaba da zama a Manchester United.

Sai dai ten Hag ya ce dole ne dan wasan bayan na Ingila ya fafata domin dawo da matsayinsa a kungiyar.

Maguire wanda aka fara da shi a wasan firimiya takwas kacal a kakar wasan da ta gabata, ya shirya komawa West Ham amma cinikin na fam miliyan 30 ya warware.

Dan wasan bayan na Ingila, mai shekara 30, yana son sake buga wasa akai-akai, kuma kocin United Ten Hag ya ce ya kamata ya yi yunkurin amfani da duk damar da zai samu.

Maguire, wanda ya yi fama da rashin buga wasanni sosai a kakar da ta gabata, an cire shi daga mukamin kyaftin din kungiyar a watan Yuli wanda tun watan Janairun 2020 yake rike da shi.

Ya kasance dan wasa da ba a yi amfani da shi ba a nasarar da United ta yi a kan Wolves a gasar Firimiyar ranar Litinin.