✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na ji bugun zuciya lokacin da aka dora mini kyamara a fim dina na farko – Abba Zaki

Mene takaitaccen tarihinka?                                             …

Mene takaitaccen tarihinka?                                             

Sunana Abba Ali Zaki, amma an fi sanina da Abba Zaki, an haife ni a Kano a watan Agustan 1989. Na yi makarantar firamare da sakandare a Intercontinental School da ke Kano, na yi digirina a fannin Nazarin Addinin Musulunci a Jami’ar  Jihar Gombe, inda na yi hidimar kasa a Jihar Benuwai daga shekarar 2015 zuwa 2016.

Me ya ja hankalinka ka shiga wannan harkar ta fim?

A gaskiya tun kafin in shiga jami’a ina da ra’ayin shiga harkar fim, amma asali ba ma fim na fara sha’awa ba, waka nake sha’awar yi, inda tun a lokacin nake rera wakoki, wannan ina maganar shekarar 2006 ke nan, wakokin da nake yi sun shafi na soyayya da na bikin aure da siyasa da sauransu, na fara sha’awar fim a lokacin da nake mataki na 300 a  jami’a,  kuma na fara alaka da ’yan fim sosai.

Kodayake a lokutan baya an yi fina-finai masu yawa a gidanmu, sai dai a lokacin abin bai shiga raina ba, sai a shekarar 2013, a wannan shekarar ana yajin aiki, sai na bar Gombe na dawo Kano, shi ne na zauna da wadanda suke harkar fim, daga nan kuma ya shiga raina.

Da wane fim ka fara?

Na fara da wani fim mai suna ‘Wani karni’, an dauki fim din a garin Jos ne, inda fim din ya kunshi su Ali Nuhu da Zaharaddeen Sani da sauransu.

Yawanci a nan Arewa idan mutum ya yanke shawarar shiga harkar fim, za a rika yi masa wani kallo haka, ko a yi yunkurin hana shi, ko ka fuskanci makamantan wadannan matsaloli daga wurin ’yan uwa ko iyaye da abokai?

A gaskiya ban fuskanci ire-ire matsalolin da ka ambata ba, a gaskiya ko lokacin da nake harkar wakokina sosai na yi albam na bidiyo kuma an yaba mini har a cikin gidanmu, lokacin da na fara waka ma na yi tunanin  mahaifina zai hana ni, inda bayan ya saurari wakar ne ya ji ma’anarta sai ya ji dadi, ya ce duk a cikin ’ya’yansa 20 ni kadai ne nake da baiwar waka, ya ce waka baiwa ce, ba abin a bata rai ba ne, kafin Allah Ya yi masa rasuwa ma ya ce zai rika taimaka mini, haka mahaifiyata. Ita shawararta ita ce in rika kare kaina, amma ita ma ta ba ni goyon baya.

Zuwa yanzu ka yi fina-finai kamar nawa?

Na yi fina-finai kamar 20, misali daga cikinsu shi ne ‘Wani karni’ da ‘Mu’assab’ da ‘Kwanan Keso’ da Make Room’ da sauransu.

Bayan ka shiga harkar fim, wane kalubale ka fuskanta ko kake fuskanta a yanzu?

Matsalolin da na fuskanta su ne yadda zan fuskanci harkar fim, ka san duk wani abu da aka ce sabo ne ka fara shi, to dole sai a hankali za ka rika gane shi, to ni ma farkon fara fim dina wannan matsalar na fuskanta, amma sannu a hankali na fahimci yadda harkar take a yanzu. 

Lokacin da aka fara dora maka kyamara yaya ka ji?

Tun kafin ma a dora mini kyamara yayin daukar fim dina na farko mai suna ‘Wani karni’, take na ji bugun zuciya, a lokacin da zan yi fitowata ta farko, sai na ga dandazo mutane suna kallona, a tunanina shi ne ko za a bar ni, ni kadai ne, wato daga ni sai mai daukar fim din ko darakta, sai na ga kowa na kallona, kuma fitowar ta farko ma taba sigari zan sha, kuma ban taba shan taba a rayuwata ba, haka na daure na bayar da abin da darakta yake bukata, daga nan kuma na ci gaba da samun kwarewa har zuwa yau. 

Wane buri kake so ka cimma a harkar fim?

To ni dai burina a ce yau Abba Zaki ya zama babban jarumin da duniya za ta san shi, wato ba wai a Najeriya kawai ba, a’a, duk duniya. 

A cikin mutanen da ka yi aiki da su, wanne ka fi jin dadin aiki da shi?

A gaskiya duk wadanda na yi aiki da su, na ji dadin aiki da su, sun ba ni hadin kai da gudunmawa sosai wajen ganin na yi aiki yadda ya kamata.

A cikin fina-finan da ka yi wani rol ne ya fi ba ka wahala da kuma wanda ka fi so?

Rol din da ya fi ba ni wahala, na kuma fi so shi ne na fim din ‘Make Room’, saboda na taka babban rol ne, na fito a fim din a matsayin mara tsoro, kuma mai jajircewa da kuma tausayi. Fim ne da aka yi shi a kan ta’addanci.

Wanda ya fi ba ni wahala ma, shi ma a fim din ‘Make Room’ ne, domin aikinsa ba irin wanda na saba gani ba ne, sai ka ga a kwana daya an yi daukar fitowa daya ko biyu, kuma fitowa daya sai ka ga an maimaita  daukarta fiye da 13, hakan ya ba ni wahala sosai. 

Za mu so ka yi mana karin bayani kan takaimaiman matsayin da ka taka a fim din ‘Make Room’ da ya ba ka wahala?

Na taka matsayin Bulus ne, kuma Bulus wani saurayi ne da ke garin Maiduguri, wanda iyayensa suka mutu, inda yake zaman kansa, yake yi wa kansa komai, yana aikin karafu da kuma kere-kere.

Wace fitowa ce ta fi burge ka a fim din?

Fitowar da ta fi burge ni ita ce, a lokacin akwai mataimakin shugaba a cikin sansanin ’yan ta’adda, inda a lokacin bayan ’yan ta’addar sun kama mu sun kai mu sansaninsu ne, shi mataimakin shugaban nasu ana kiransa ‘Banza’, akwai fitowar da nake yi da shi, a lokacin yana daukar matata, za su tafi da ita da karfi, inda nake zuwa in tare gabansa, abin da ya burge ni, kowa yana tsoronsa, amma mu sababbin zuwa ne, amma har na yi jan wuya na tsaya a gabansa, har na kwace matata.

Wanda ya fi ba ka wahala fa?

Fitowar da na rika gudu kamar raina zai fita a lokacin da ’yan ta’adda suke kokarin kashe ni, dalilin da ya sa na fi shan wahala kuwa shi ne, na yi gudu sosai, kuma a lokacin ina azumi, a karshe dai suka kashe ni bayan sun sa mini taya suka kona ni.

Me za ka ce game da lokeshan da ma’aikatan da suka dauki wannan fim din, kasancewa ka ce ya bambanta da sauran fina-finan da ka yi?

A gaskiya ban taba ganin irin lokeshan din fim ba, wanda zan iya cewa a Hausa fim ma ba a taba yin fim kwatankwacin irinsa ba, saboda kayan aikinsu da yanayin aikinsu gaba daya, saboda an gayyato Turawa daga kasashen waje, wadansu ma’aikatan kuma daga Kanada da kuma Afirka ta Kudu. 

Kuma ba sa yin sauri, komai daki-daki ake bin sa, ba a damu a shafe rana guda ana daukar fitowa daya ba, su dai damuwarsu idan wannan daukar ta yi kyau, kuma ta bayar da abin da ake so, to shi ke nan. 

Kuma Daraktan fim din Roberts Peters da kuma furodusa din Rogers Ofime mutane da suka san darajar dan Adam, kuma suna da saukin kai da kuma dadin sha’ani.