✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na gina gida daga sayar da lemo da ayaba – Abba Gadara

Wani dan kasuwa mai sayar da kayan marmari a kofar shiga ginin Sakatariyar Gwamnatin Jihar Bauchi ya ce ya samu rufin asiri sosai ta sanadiyyar…

Wani dan kasuwa mai sayar da kayan marmari a kofar shiga ginin Sakatariyar Gwamnatin Jihar Bauchi ya ce ya samu rufin asiri sosai ta sanadiyyar kasuwancin lemo da ayaba da kankana da gwanda da sauran kayan lambu.
Abba Gadara ya ce: “Na samu rufin asiri daidai gwargwado a sanadiyyar wannan kasuwanci mai albarka. Na gina gidan kaina kuma yanzu haka ina da mata uku da ’ya’ya takwas.”
Ya ce tun yana Jihar Kano yake kasuwanci kafin daga bisani ya dawo Jihar Bauchi. Kuma ya ce yana da dimbin yara wadanda yake koya wa kasuwancin lemo da ayaba.
Daga nan ya bukaci matasa su tashi tsaye, inda ya ce  “ babu wata al’umma da za ta samu ci gaba matukar matasa suna zaman kashe wando. Yanzu an wuce lokacin da matasa za su dogara da aikin gwamnati dole sai wadansu sun shiga kananan sana’o’i da kasuwanci wadanda su ne suke bunkasa tattalin arzikin kowace kasa a duniya.”
 A karshe ya ce babbar matsalar da ake fuskanta a halin yanzu ita ce ta rashin ciniki da rugujewar tattalin arzikin mutane. Ya ce “Galibin mutane yanzu  ba sa iya cin abinci sau biyu a rana sakamakon dimbin matsaloli da suka addabi kasar nan.”