✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na gina gida da sana’ar masa –Hajiya Fatima

Hajiya Fatima mace ce da ta fara sana’ar tuyar masa tun kafin ta yi aure.  A lokacin da take zantawa da Aminiya a garin Gombe…

Hajiya Fatima mace ce da ta fara sana’ar tuyar masa tun kafin ta yi aure.  A lokacin da take zantawa da Aminiya a garin Gombe ta bayyana  yadda sana’ar ta rufa mata asiri. Ga yadda tattaunarwar ta kasance:
Aminiya: Za mu so mu ji lokacin da kika koyi sana’ar tuyar masa?
Eh, na fara wannan sana’a ta tuyar masa ce tun a shekarar 1992 wato kimanin shekaru 24 da suka gabata ke nan. Tun ina yi a cikin gida lokacin bai wuce mudu daya zuwa biyu nake toyawa ba, ana zuwa ana saya kafin jarina ya yi karfi na kama shago, inda yanzu haka nake toya mudu 25 a kowacce rana kuma ya kare tas. Har ila yau, na koyi wannnan sana’a ce a wajen mahaifiyata.
Aminiya:  Akwai wata sana’a da kike yi bayan wannan?
Bayan tuyar masa da nake yi yanzu haka na fara hadawa da sayar da abinci, inda yanzu na kama Shago shi ma ya karbu, ba laifi. Jama’a suna saya kuma a gaskiya asirina ya rufu ba ni da wata matsala ta harkar rayuwa saboda yadda wannan sana’a ta rufa mini asiri har gida na gina da kaina da wannan sana’a. Har ila yau, na sayi motar hawa na sayi injin markade da keken dinki biyu da firji da babura guda biyu wadanda ake mini haya da su.
Aminiya: Baya ga sayar da masar dai-dai akwai masu zuwa suna saya don biki?
Eh, ana ba ni kwangila na yin masa na masu bikin aure da suna mutum shi zai sa yi komai da komai nasa ya kawo mun na yi musu masa, su biya. Kodayake, ni ba na kayyade abin da za a ba ni duk abinda aka ba ni karba nake yi, na sa musu albarka.
Aminiya: Akwai wasu kalubale da kike fuskanta?
A gaskiya akwai kalubale domin komai ruwan sama ko dari bai taba hana ni na fito inyi sana’a ta ba, saboda  duk idan wata rana zan yi wata rana inyi fa shi sana’ar ba za ta dore ba, kuma babu wani wanda ya taba zuwa ya taimakamin duk da cewa gwamnati a baya tana taimakawa masu kananan sana’o’i.
Aminiya:  Ko kina da wani kira ga ’yan uwanki mata game da muhimmancin sana’a?
Kiran da zan yi wa mata shi ne su tashi tsaye sosai wajen neman na kansu tun da sauran karfinsu don samun hanyar dogara da kansu da hakan zai ba su dama don taimakawa gida. Ba lailai sai maigida ya kawo ba saboda halin rayuwa ka ga kamar ni hatta maigidana yana cin moriyar wannan sana’a tawa domin ina rage masa wasu dawainiyoyi na yau da kullum.