✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na gina gida da sana’ar gyaran janareta – Sulaiman Usman

Wani matashin mai sana’ar gyaran janareto a Jihar Gombe Injiniya Sulaiman Usman ya bayyana sana’ar gyaran janareta da cewa da ita ya gina gida har…

Wani matashin mai sana’ar gyaran janareto a Jihar Gombe Injiniya Sulaiman Usman ya bayyana sana’ar gyaran janareta da cewa da ita ya gina gida har ya yi aure.
Injiniya Sulaiman Usman, ya ce ya fara koyon wannan sana’ar ce tun kimanin shekara 19 da suka gabata wanda yanzu haka shi ma yana da yara guda takwas wadanda suke karkashinsa baya ga guda biyar da ya yaye suke cin gashin kansu yanzu.
Da yake bayyana irin rufin asirin da ya samu a dalilin wannan sana’a ta gyaran janareto Injiniya Sulaiman cewa ya yi duk wani rufin asiri da dan Adam yake nema a rayuwa ya samu sai dai godiya ga Allah, “domin yanzu ma aiki ba ya yanke mini saboda yadda nake kamanta gaskiya a tsakanina da kwastomominsa,” inji shi.
Ya kuma ce a shekarun da ya share yana wannan sana’a babu janareton da za a kawo masa ya gagareshi gyarawa, “sai dai ya wahalar da ni, amma daga karshe zai gyaru.”
Ya ce idan ya samu tallafi daga wajen gwamnati ko wata kungiya zai iya fadada masana’antarsa ya dauki yara masu yawa wadanda za su koyi sana’ar su tsaya da kafafunsu har wasu ma su ci gajiyar su a gaba.
Har ila yau, ya kara da cewa wani rufin asairin ma shi ne da wannan gyara yake daukar nauyin karatun ’ya’yansa yake kuma taimakawa iyayensa da ’yan uwa har ma wasu al’umma da suke cin moriyar wannan sana’a tasa domin yana kyautatawa abokan hulda na yau da kullum.
Daga nan ya yi kira ga matasa wajen cewa su daina raina sana’a domin a sana’a babu karama duk yadda mutum ya dauke ta haka za ta bi da shi.
Ya kuma ce duk da wani lokacin ana samun wutar lantarki jifa-jifa bai rasa aiki domin akwai wadanda ko akwai wuta suna son janareton su ya zama bai da matsala wanda da an dauke ta sai su kunna, a wani lokaci kuma ana kawo wutar ne mara karfi.
Ganin ya samu ribar wannan sana’a ya yi fatan hatta ‘ya’yansa idan suka taso su gaje shi. “Sai dai wanda ya girma ya ga zai canja sana’a wannan kuma shi ya zabawa kansa haka, amma shi zai so koda daya daga cikinsu wani ya gajeshi,” inji shi.
Daga nan sai ya nemi gwamnati da ta tallafawa masu sana’o’in hannu irinsu don kara samun matsaya saboda duk wata harka da mutum yake yi sai da tallafi mai karfi kafin ya tsaya da kafarsa.