✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na gargaɗi Ningi kan zargin cushen N3.7trn a Kasafin Kuɗin bana — Ndume

Ndume ya ce su Sanatocin Arewa za su tsaya wa Arewa, babu yadda za a yi a cuci Arewa suna kallo.

Mai Tsawatarwa a Majalisar Dattawan, Sanata Mohammed Ali Ndume, ya ce ya gargaɗi Sanata Abdul Ningi kan zargin da ya yi na cewa an yi cushen maƙudan kuɗaɗe a Kasafin Kuɗin bana.

Sai dai ya bayyana takaicin cewa duk da gargaɗin da ya yi Sanata Ningi bai karɓi shawararsa ba.

A ranar Talata ce dai Majalisar Dattawa ta dakatar Sanata Ningi wanda ke wakiltar Bauchi ta Tsakiya na tsawon watanni uku saboda zargin da ya yi na cewa majalisar ta yi cushen Naira tiriliyan 3.7 a Kasafin Kuɗin bana.

A wata hira da ya yi cikin Shirin Siyasa da Gidan Talabijin na Channels a ranar Laraba, Ndume ya ce Sanatan Bauchi da aka dakatar bai yi daidai da ba kuma zargin da yake yi babu kamshin gaskiya a cikinsa.

“Na zauna da Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, kuma ya fusata sosai kan abin da Ningi ya yi,  amma maganar gaskiya ni ma ban ji daɗi ba. Abin da ya yi Sanata Ningi ya yi bai dace ba, saboda na shiga cikin zargin,” in ji Ndume.

“Tun farko dai wannan taƙaddama ta fara ne zargin cewa kaso mafi rinjaye na manyan ayyuka a Kasafin Kuɗin ya karkata zuwa Kudu.

“Na gaya masa [Ningi] cewa ya yi kuskure. Har ma na gargaɗe shi lokacin da ya kawo min maganar. Na gaya masa ya sami wanda zai yi nazarin kan kasafin kuɗi. Amma ya ƙi ya sauraro na.”

Ndume ya ce, Ningi na ƙoƙarin mayar da lamarin Kasafin Kuɗin 2024 tamkar wani batu na ƙabilanci da banbancin siyasa, wanda a cewarsa hakan ba daidai ba ne.

Sanata Ndume ya ce lokacin da Ningi ya fara gabatar masa da ƙorafin, sai ya nemi ya kawo hujjoji amma ya gaza.

Ndume ya bayyana cewa a matsayinsa na ɗaya daga cikin Sanatocin Arewa, zai iya tabbatar da cewa babu wani fifiko da aka bai wa Kudu fiye da Arewa a Kasafin Kuɗin sabanin yadda Ningi ya yi iƙirari.

Ana iya tuna cewa, a tsokacin da Sanata Ndume ya yi yayin zaman majalisar na rana Talata, ya ce suna fatan Ningi zai gane kuskuren sa ya rubuta wasika ta bada hakuri.

Ndume ya ce Sanatoci Arewa ba su ki shi ba, amma su dattawa ne.

Ndume ya ce su Sanatocin Arewa za su tsaya wa Arewa, babu yadda za a yi a cuci Arewa suna kallo.

Ndume ya ce daga Majalisar Wakilai har na Dattawa, ’yan Arewa ne suka fi yawa. Saboda haka za su tsaya wa Arewa.

To sai dai biri ya yi kama da mutum, domin Sanata Jarigbe Agom Jarigbe na Jihar Kuros Riba ta Arewa, ya ce wasu sanatoci sun samu Naira Miliyan 500 kowanne daga cikin Kasafin Kuɗin na bana.

Jarigbe ya ce “idan muna son shiga cikin wannan batu, dukkanmu muna da laifi, wasu sanatoci suna da wannan dabi’ar.

“Ni ina da tabbacin cewa manyan sanatoci sun samu Naira miliyan 500 kowannensu, in batun manya ne, ni ma babban Sanata ne, amma ba a ba ni ba.”