Angela Okorie, ’yar wasan da ta fara shirin fim a 2009, wacce kuma a baya ta kasance tauraruwar tallata sabulun Delta ta bayyana yadda ta gamu da abin da ake kira kauna a kasar Amurka.
’Yar wasan, wacce ya zuwa yanzu ta fito cikin fina-finai sama da 50, ta bayyana cewa babu shakka ta samu nasara a sana’arta, musamman kuma ta nuna yadda take da masoya a fadin duniya gaba daya.
Kamar yadda aka tambaye ta ko me za ta ce game da masoyanta da ta ce suna ko’ina a duniya, sai ta fara bayanin cewa:
“Zan iya tunawa, na gamu da abin da ake kira kauna ta hakika a birnin New York na Amurka, inda wata rana na je yin sayayya wani kanti; kawai sai ga wani kyakkyawan saurayi ya tunkare ni kai tsaye. Ya nuna mini matukar kauna, sannan ya ce ya yi matukar mamaki da ya hadu da ni ido-da-ido. Ni kuwa mamaki ya kama ni, inda na samu kwarin gwiwa na tambaye shi ko dalilin me ya sa ya fadi haka? Shi ne ya ce a duk cikin ’yan fim babu wacce yake kaunar ganin fuskarta sai ni. Ni kuwa na yi masa godiya, na ce ya ci gaba da kallon fina-finaina. Bai bar ni haka nan ba sai da ya nemi in rubuta masa sa hannuna. Ni kuwa na rubuta masa ba tare da bata lokaci ba.” Inji ’yar wasa Angela.
Na gamu da kauna a Amurka -’Yar fim Angela Okorie
Angela Okorie, ’yar wasan da ta fara shirin fim a 2009, wacce kuma a baya ta kasance tauraruwar tallata sabulun Delta ta bayyana yadda ta…