✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na fito takara ne don ceto ’yan uwana mata – Jamila Abubakar

Yayin da harkokin siyasa ke ta kankama don fuskantar zaben badi ’yan siyasa na yunkurawa don fara gwagwarmayar neman mukamai. Hajiya Jamila Abdullahi Abubakar Tarauni,…

Hajiya Jamila Abdullahi Abubakar TarauniYayin da harkokin siyasa ke ta kankama don fuskantar zaben badi ’yan siyasa na yunkurawa don fara gwagwarmayar neman mukamai. Hajiya Jamila Abdullahi Abubakar Tarauni, daya daga cikin matan da suka nuna sha’awar fitowa takarar shugabar mata ta Jam’iyyar APC ta Jihar Kano ta shaida wa Aminiya cewa makasudin takararta shi ne don ta tallafa wa mata ’yan uwanta:

Aminiya: Wane shiri kike yi don tunkarar takararki a zaben shugabannin Jam’iyyar APC ke gabatowa?
Hajiya Jamila: Makasudin tsayawa ta takarar shugabar mata a Jam’iyyar APC kuma ta Jihar Kano, shi ne muna son mu bayar da gudunmawarmu ne ga mata ’yan uwanmu kuma mu ci gaba da wayar musu da kai don su zo mu hada karfi da karfe mu tafi tare, saboda a samu a fid da jaki daga duma.
Aminiya: Ta wane bangarori kike ganin ya kamata a taimaki mata ko jama’a?
Hajiya Jmaila: To abin da nake nufi da a fid da jaki daga duma shi ne, mu mata muna bayar da gudunmawarmu dari bisa dari a harkar siyasa kuma da mata ake yin komai na harkar zabe, amma idan an ci zaben sai ka ga an bar matan a gefe. Don haka muke wayar musu da kai a game da yadda za su shiga cikin jam’iyyar nan mu yi aiki da ilimi da basira ta hanyar da ba ta saba wa addini ba, mu taimaka wa iyaye mata. Akwai masu marayu, akwai wadanda ba su da karatu ba su da yadda za su shiga ciki su yi harkar. Ana ganin kamar mace ta shiga harkar siyasa ba ta da daraja, to yanzu abin ya canja. To shi ya sa muka shiga ciki muke kira ga ’yan uwanmu mata mu tashi mu taimaka wa junanmu da ’ya’yanmu da ’ya’yanmu da iyayenmu da karfinsu ya kare.
Aminiya: Shugabar mata a jam’iyya ba matsayi ne na gwamnati ba, ta yaya za ki iya taimaka wa matan?
Hajiya Jamila: Idan har Allah Ya kai ni wannan kujera, ai Ya kai ni inda zan taimaka wa ’yan uwana mata saboda duk abin da za a yi a jam’iyyance ina ciki. Kamar yadda muke rokon Allah kuma muke ganin Insha Allahu da taimakon Ubangiji za mu kafa gwamnati a kasa da Jihar Kano, zan kai kukan ’yan uwana mata. Jihar Kano na da kananan hukumomi 44, kuma kowace karamar hukuma da akwai wakilai mata, ko su suka tsaya suka yi wa jam’iyya aiki muka tsaya a kansu aka kai kokensu aka dora su a kan tafarkin alheri da tallafi, za su samu alheri kuma za su taimaka wa iyalansu da sauran matan karkara.
Aminiya: Koyaushe ku mata kukan ce ku ne a kan gaba wajen yin zabe, amma kuna ta koke-koke. Shin ba ku gamsu da gudunmawa ko tallafin da ake ba ku ba ne?
Hajiya Jamila: To yadda wasu suke ganin kamar mata ba sa gamsuwa, babu abin da za mu ce ga gwamnatin Jihar Kano kan tallafi da tsare-tsaren kula da mata sai godiya. Gwamnan Kano ya tallafe mu dari bisa dari ya goya mu, ya nuna mana shi uba ne. Saboda ya ba mata tallafi kuma ya kai wasu ’ya’ya mata karatu. Wasu za su zama likitoci, wasu malaman jinya, wasu za su koyo kimiyya da sauran fannoni. Haka a cikin karkara da birni ya ba mata jari, don haka sai dai mu ce alhamdu lillahi. Haka muna da mata kwamishinoni kuma duk suna kokari a kan sha’anin ’yan uwa mata kuma suna ba su agaji daidai gwargwado.
Aminiya: Wane kira za ki yi ga ’yan uwanki mata?
Hajiya Jamila: Ina kira su ba ni goyon baya domin na taba rike mukamin shugabar mata amma ina tare da wani dan takarar Gwamna a lokacin wanda wannan ma ya hade kananan hukumomi 44, inda na yi wa wannan dan takarar shugabar mata yakin neman zabensa. Kuma a wancan lokaci matan sun ga irin gudunmawar da muka ba su. Kuma a wannan fitowa da muka yi ba ta kanmu ba ce mu kadai, matan ne da kansu da suka ji dadi suka ce lallai mu fito takarar, saboda a samu yadda za a yi a shigar da su cikin gwamnati, a tallafa musu.
Aminiya: Me ya sa a ganinki mata da yawa ba sa son fitowa neman mukamai?
Hajiya Jamila: To ka san kamar mu a nan Jihar Kano a baya za a iya cewa karancin ilimin mata ne, amma a yanzu mun samu wayewa kuma mun samu ci gaba domin malamanmu na ddini suna wayar mana da kai cewa akwai mu’amalar da mace za ta yi a harkar aiki ko harkar zabe idan za ta tsare mutuncinta.
Idan har za ki tafiyar da al’amuranki ba tare da kin saba wa addini ba, babu wani abin damuwa.  A da ana yi wa siyasa wata fassara, amma yanzu idan an duba ai siyasa ta masu ilimi ce.