✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na fi shekara 30 ina harkar zogale -Maman Ladi

“Tun kafin masana ilmin kimiyya su gano kuma su yi bayanin cewa zogale ba wai kadai abincin Hausawa ba ne, a’a, yana ma yin maganin…

“Tun kafin masana ilmin kimiyya su gano kuma su yi bayanin cewa zogale ba wai kadai abincin Hausawa ba ne, a’a, yana ma yin maganin ciwurwuka har 90, nake cikin wannan sana’a ta sarrafa shi da sayar da shi. Bukatar ruwan zogale ta kai wani matsayi, inda ta yi tashin gwauron zabi, alhalin abin da ake zubarwa ne a da, amma daga baya ya zama abin da aka fi kauna, musamman tun daga tsakanin Turawa da ’yan boko da sauran jama’a”.
Wannan wani tsokaci ne na wata dattijuwa mai suna Salamatu Shu’aibu, wadda aka fi sani da Maman Ladi, a wata tattaunawa da ta yi da Aminiya kwanan baya.
Dattijuwa Maman Ladi, wacce take zaune a arewacin layin Abuja na Rigasar Kaduna, amma tana sana’arta ce a kan titin Ahmadu Bello, a daidai ofishin Alhaji YA Ahamed, ta ce ta fara baje kolinta na zogale ne a gefen masallacin kamfanin New Nigerian, kimanin fiye da shekaru talatin da suka gabata.
“Yayin da tafiya ta yi nisa da kuma saboda rashin jama’a, sai na koma kofar kamfanin, a gefen titi, sannan na koma kofar kamfanin jiragen sama (Nigera Airways), wanda bayan ya mutu, sai na komo nan inda nake a yanzu, kimanin shekaru goma ke nan”, inji ta.
Wani abin sha’awa da Maman Ladi ta ce ba ta mantawa shi ne a zamanin mulkin Janar Buhari lokacin “yaki da rashin da’a” da ake korar mutane masu talla a gefen titi. Ta ce, “A lokacin da sojoji sun zo kora, suka ga zan kwashe kayan sana’ata, sai su ce: “Mama ki zauna, ba ruwanmu da ke”.  Sai kuma wani karatu da ’yan tasha suka taba koya mata. Ta ce wasu mutum biyu ne suka zo suka ce mata suna jin yunwa, amma Naira 30 suke da shi. Ta tausaya musu ta ba su zogalen Naira dari, ta bar su a zaune, ta tafi sallah, kafin ta dawo sun yi mata karkaf sun sace mata kudi. Tun daga ranar ba ta kara barin kudinta cikin kayan sana’arta ba, in za ta je yin sallah.
Maman Ladi ta ce takan ajiye kayan sana’arta, kamar bokitai da kwanoni da kwando a wani gefe na ofishin attajiri Alhaji YA Ahamed, “Wanda bai taba bata fuskarsa a kan haka ba. Hasali ma yakan saya wa iyalansa zogalan, har zuwa lokacin da ya rasu, Allah Ya jikansa, sannan ’ya’yansa ba su hana na ci gaba da aje kayana ba”. Inji ta.
A dangane da ko me ya sa ba ta da ’yar aiki, sai ta ce ba ta son ’ya’ya da jikokinta su saba da kudi. ’Yarta na karatu a Sakandaren Maimuna Gwarzo, sannan jikarta na karatu a firamaren Askolaye.
Ta ce wani direban Baturen Ingilia mai suna Mista Samuel Ojo, ya yi mamakin lokacin da maigidansa Arthur Brookes ya ce ya sayo masa zogale. Da ya tambaye shi sirrin, sai ya ce masa ai abinci ne kuma magani. “Ai mu tubarkalla, abin da ake zubarwa a da, yanzu ya zama kudi, domin kwalbar ruwan zogale na kamawa daga Naira 120 zuwa Naira 350”. Inji ta.