✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Na dauki siyasa a matsayin addini —Shekarau

Shekarau ya ce siyasa ita ce addininsa, kuma addininsa shi ne siyasa.

Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Kano ta Tsakiya, Sanata Ibrahim Shekarau, ya ce ba zai taba daina siyasa ba sai in mutuwa ce ta dauke shi domin kuwa ya dauke ta a matsayin addini.

Tsohon gwamnan na Jihar Kano ya yi wannan furuci ne yayin ganawa da manema labarai bayan kaddamar da Majalisar Shura a gidansa da ke Unguwar Mundubawa a birnin Kano.

Shekarau, wanda ya yi gwamnan Kano tsawon wa’adi biyu kuma ya zama Ministan Ilimi a gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, ya ce “ba ni da lokacin da zan yi ritaya daga siyasa har sai na mutu.”

Shekarau ya kaea da cewa, “Dalilin da ya sa nake maimaita wannan batu shi ne, babu wani lokaci da zan yi ritaya daga siyasa.

“Fiye da tsawon shekara 20 ina fadin haka, siyasa ita ce addinina, kuma addinina shi ne siyasa.

“Saboda haka babu wani lokaci da zan bar wannan addini saboda dukan su biyu suna aiki kafada-da-kafada da juna ne.

‘Bautar Allah ce’

“Addini shi ne bauta wa Allah kuma mafi kololuwar bautar Allah ita ce hidimta wa al’umma wadanda Allah ne ya halicce su.

“A mahanga ta addinin Islama, duk wanda ka taimaka wa, kana bin umarnin Allah ne.

“Idan na yi wa wani addu’a, ko na kyautata masa, hakan wani nau’i ne na bautar Allah.

“Saboda haka ita siyasa babu abin da ta kunsa face yi wa al’umma hidima, kuma ba sai lallai mutum yana rike da wani mukami ba.

“Ko shekara 90 na kai ta yadda tsufa ba zai bari na tsaya takara ko fita yawon yakin neman zabe ba, zan iya bayar da shawara ga jama’a ina kwance a bisa gado.

“Saboda haka ita siyasa wata hanya ce ta yi wa mutane hidima, kuma [wannan] ita ce fahimta kuma akidar da na rika.

“Dalilin haka nake tausayin duk wanda yake tunanin ritaya daga siyasa, kila sai dai bai fahimci ko mece ce siyasa ba.

“Kasancewar galibi suna iyakance ta ne kadai da samun wani mukami, wadanda suka fahimci cewa idan ba wannan ba to mutum ba siyasa yake ba.

“To a gaskiya masu irin wannan tunani ba su fahimci hakikanin abin da ake nufi da siyasa ba.

“Abin da na fahimta da siyasa shi ne samun damar yin mu’alama da jama’a da kuma hidimta musu ta kowacce hanya.

“Kuma in dai wannan ne babu lokacin da zan daina face ajali ne ya yi kira na.

“Ina fadin haka ne saboda na fahimtar da masu adawa da ni da ke yada jita-jitar ko kuma masu neman su debe wa magoya bayana tsammani [da] cewa Sardaunan Kano ya kusa ritaya.

“Wasu ma suna cewa ba zan sake tsayawa takara ba, sai dai wannan ba maganar da ke gabanmu ba ke nan don har yanzu ina da sauran shekara biyu kafin na kammala wa’adi na kuma wannan wata dama ce a gare ni”.