Ma’aikatar Jinkai da Kai Agajin Gaggawa ta Tarayya ta sanar da bude shafinta don sake daukar rukuni na uku na matasa cikin shirinta na N-Power daga ranar Juma’a, 26 ga watan Yuni.
Shirin dai Gwamantin Tarayya ce ta bullo da shi tun a shekara ta 2016 da zummar rage radadin talauci musamman ga matasa da suka kammala karatu.
Yayin da matasa suka dukufa wajen fara yin rijistar, Aminiya ta zakulo wasu muhimman abubuwa da ya kamata a kula da su da zarar an fara rijistar.
Za a bude shafin ga duk wadanda suka cancanta da misalin karfe 11:45 na daren ranar Juma’a 26 ga watan Yuni.
- Za a fara daukar sabbin ‘yan N-Power — Minista
- Gaskiya ne ba mu biya ‘yan N-Power 12,000 hakkokinsu ba — Gwamnati
Yin rijistar kyauta ne kyauta ne kuma ba a biyan ko sisin kwabo, sai dai ana bukatar mai yin rijistar ya kula da wadannan ka’idojin:
- Wadanda suke tsakanin shekaru 18 zuwa 35 ne kadai suka cancanci su yi rijista a shirin (wato wadanda aka haifa tsakanin shekarar 1985 zuwa 2002).
- Kafin ka fara yin rijistar, ka tabbata ka tanadi wadannan abubuwan:
- Takarda mai dauke da cikakkun bayanai na lambar rijistar banki (BVN)
- Karamin hoto wanda nauyinsa bai wuce 1mb ba
- Lambar waya ko adireshin ‘e-mail’ mai aiki
- Takardar shaidar kammala yi wa kasa hidima (NYSC) ga wadanda suka kammala digiri kuma suke son shiga tsarin N-Teach da kuma N-Health.
- Da zarar an bude shafin, sai ka shiga npower.fmhds.gov.ng don fara rijistar.
- Idan shafin ya bude za a bukaci ka karanta sharudda da ka’idojin shirin kuma a bukaci ka amince da su.
- Sai ka shigar da lambar wayarka ko adireshin ‘e-mail’.
- Daga nan za a mayar da kai akwatin ‘e-mail’ dinka don tabbatar da sakon da aka turo maka.
- Da zarar an tabbatar da adireshin ‘e-mail’ din naka sai ka saka labar BVN dinka da kuma kwanan watan haihuwarka. Amma idan bayananka na cikin lambar BVN din ba daidai suke ba, ba za a bari ka ci gaba ba.
- Sai ka cike sunanka ta hanyar saka sunan farko da suna na biyu. Kamar yadda yake a jikin lambarka ta BVN
- Daga nan sai ka cike matsayin karatunka, ka cike in ka yi makaranta ko a’a
Shirin N-Power kowanne matakin karatu mutum ya keda shi zai iya cikewa.
Daga nan za a bukaci ka dora shaidar kammala bautar kasa ga wanda ya kammala digiri.
- Sai kuma a bukaci ka dora shaidar katin zama dan kasa ko wani katin shaida na gwamnati.
Takardun da aka amince za a iya amfani da su sune katin tafiye-tafiye, katin zama dan kasa, lasisin tuki ko kuma katin zabe.
Daga nan za a baka dama ka yi nazari na tsanaki a kan bayanan da ka shigar kafin ka tura.
Idan ka je wurin turawar, za a baka wata lambar shaida wadda taka ce kai kadai, ka rubuta ta a takarda ka adana ta.
Ma’aikatar Jinkan dai ta sanar da cewa za ta sallami rukunin farko na ‘yan N-Power ranar 30 ga watan Yunin da muke ciki, yayin da rukuni na biyu za a sallame su ranar 31 ga watan Yuli mai kamawa.
Tun daga kirkirar shirin dai a shekara ta 2016 zuwa yanzu an dauki mutane dubu dari biyar.
An dauki mutane 200,000 a rukunin farkon shirin cikin shekara ta 2016, sai kuma mutane 300,000 na rukuni na biyu da suka fara a watan Agustan 2018.