Wani mazuru ya yi matukar sa’a inda ya tsira da rayuwarsa bayan ya yi kwana 52 a kulle a cikin wani kangon gidan da aka yi watsi da shi a wata unguwa da ke birnin Blaardingen a kasar Netherlands.
Muzurun ya rika cin takardu da fafutikar neman hanyar samun ruwa don tsira da ransa kafin a ceto shi.
A karshen watan Agusta ne sababbin wadanda suka mallaki gidan a Blaardingen suka yi mamakin ganin muzurun a cikin wani yanayi na jin yunwa, yayin da suka bude kofar gidan nasu.
Sun sayi gidan ne bayan an yi gwanjonsa, kuma sun bude kofar ce a karo na farko da suka taka kafarsu a gidan.
An tuntubi masu samar wa dabbobi masauki a Blaardingen kuma sun kama muzurun suka fara bincike.
Sai dai an samun rahoton cewa, tsohon mamallaki muzurun ya bar gidan tun a ranar daya ga Yulin bana, kuma ana jin tun daga lokacin muzurun yake ta gwagwarmayar rayuwa da kansa.
Ba a sani ba ko tsohon mamallakin muzurun ya yi watsi da shi ne, ko a gaba yana da niyyar dawowa don ya kula da shi, ko kuma wani mummunan abu ya same shi a wani lokaci, amma masu killace dabbobi na Blaardingen ba su samu alamun abincin da ya rage wa dabbar ba, idan ma akwai, na wani karamin lokaci ne da muzurun ya cinye shi kafin a ceto shi.
Abin da ya fi ba da mamaki ga masu ceton shi ne muzurun ba ya da wata hanya mafi sauki ta samun ruwan sha, don an kasa gano ta yadda muzurun yake samun ruwa, amma wadansu sun yi hasashen mia yiwuwa akwai wata kafa da yake samun ruwan sha a wani wuri a cikin gidan.
An kai muzurun da ake kira da Finn zuwa asibitin gaggawa inda aka gwada jininsa sannan aka sanya masa na’urar binciken cikinsa ta IB.
An gano cikin nasa cike yake da rubabbun takardu, wanda hakan yake nuna cewa ya yi ta cin takardu ne don tsira da ransa, kuma akwai alamun bai cin abinci mai kyau na gina jiki, sai dai da alamun yana cikin koshin lafiya.
Da alamar cewa, muzurun ya shiga cikin mayuwacin hali kafin a ceto shi, kasancewar yadda aka lura yana matukar gudun jama’a kuma yana tsoron mutane.
Likitocin dabbobi suna sa ran muzurun ya samu cikakkiyar lafiya kuma ya sake dawo da amincewa da mutane kamar yadda ya saba.
Ma’aikatan kula da dabbobi a garin Blaardingen sun ce, za a sa muzurun ya koma zama a gida tare da mutane.
Wata kungiya mai tara kudade ta kai kudi don kula da lafiyar muzurun da kuma jinyarsa da kuma tallafin da za a biya don samar masa matsuguni na tsawon makonni.
“Muna fatar rayuwar muzuru Finn za ta inganta. Dole ne koyaushe a mai da hankali da hakan bayan wannan tsawon lokaci yana raye, amma duk da haka da alama yana cikin koshin lafiya,” inji Dik Nagtegaal na Kungiyar Kare Dabbobi.
Ya ce “Finn yana dan yin tafiya, an auna nauyinsa inda sakamakon ya nuna yana da nauyin kilo 2.6 a makon jiya, bayan kula da lafiyarsa da mako guda ya kai kilo 3.
Yana samun abinci sau da dama a rana don karfafa samun ingantacciyar lafiya.