✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Zazzau: Za a yi zaman makokin kwana uku a Kaduna

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku a jihar sakamakon rasuwar Sarkin Zazzau kuma Shugaban Majalisar Sarakunan jihar, Shehu Idris. Hadimin Gwamna…

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku a jihar sakamakon rasuwar Sarkin Zazzau kuma Shugaban Majalisar Sarakunan jihar, Shehu Idris.

Hadimin Gwamna Nasir El-rufa’i a kan Karkokin Watsa Labarai, Muyiwa Adekeye ya bayyana hakan a sanarwar da ya fitar da safiyar Litinin.

Sai dai ya ce ofisoshin gwamnati za su ci gaba da kasancewa a bude kamar yadda aka saba a ranakun Litinin da Talata, yayin da ranar Laraba za ta kasance a matsayin ranar hutu domin girmama sarkin.

“Za a sauko tutoci kasa-kasa yayin wannan lokacin juyayin”, inji sanarwar.

Sarkin Zazzau marigayi Alhaji Shehu Idris ya rasu ne a asibitin sojoji da ke Kaduna yana da shekaru 84 kuma tuni aka yi jana’izarsa a fadar masarautar da ke Zariya tare da binne shi kusa da sauran magabatansa.

Daga cikin wadanda su ka samu halartar jana’izar akwai Sakataren gwamnatin Jihar Kaduna, Alhaji Balarabe Lawal Abbas, kakakin majalisar dokokin jihar, Yusuf Zailani da sauran manyan mukarraban gwamnati.

Kazalika, Shugaban Ma’aikatar Fadar Shugaban Kasa,  Farfesa Ibrahim Gambari ya jagoranci tawagar Gwamnatin Tarayya da ta kunshi Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama, Sanata Hadi Sirika, Ministar Kudi, Zainab Ahmed, Ministan Muhalli, Mahmud Muhammad da kuma Mai Taimaka wa Shugaban Kasa Kan Harkokin Watsa Labarai, Malam Garba Shehu.

Alhaji Shehu Idris wanda shi ne sarkin Zazzau na 18 ya dare karagar mulki  tun ranar 15 ga watan Fabrairun, 1975 inda ya sahfe sheakaru 45 yana mulki.