✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutuwar Mandela: kalubale ga shugabanni

Sakonnin waya Aminiya ta sauya min sunaEditan jaridar Aminiya mai farin jini da karbuwa, ina mai godiya ga yadda kuke karbar sakonnin al’umma da kuma…

Sakonnin waya

Aminiya ta sauya min suna
Editan jaridar Aminiya mai farin jini da karbuwa, ina mai godiya ga yadda kuke karbar sakonnin al’umma da kuma sadar da sakonsu. Sai dai kun canza min suna. Daga Gado Marafan Sifawa zuwa Abubakar. 08065717934.

Kaico ga alkalin gubucin Makarfi
Edita ka isar min da sakon kaico ga Alkali haruna Aliyu mai sharia, a Gubucin Makarfi Kaduna. Wannan mummunan aiki an saga talakawa, Allah Ya kiyaye gaba domin ta sace ta fito fili. Daga Sadi Sani Rano Rurum Mile 12 Legas 07060831104.

Salam Edita. Don Allah me yasa idan na turo sako ba ka bugawa, bayan kuma ni aminin Aminiya ne. Gaskiya tunda aka fara bugata guda uku kawai na rasa duk yanzu haka suna nan a gidana. Daga Adamu M. Yawale Maifarare Na’ibawa Kano  08065871836.

Jinjina ga Al-Makura
Don Allah Aminiya ku mika min gaisuwata zuwa ga Mai girma Gwamnan Jihar Nasarawa, Tanko al-Makura. Ina yi masa fatan alheri kan irin ayyukan da yake yin a ci gaban jiha. Allah Ya kara hada mu da gwamna mai adalci irinka ko bayan ba ka. Daga Bashir Yahaya Keffi. 0806920060.

Ga Dokta Mariya dantata
Hakika muna godiya ga kan yadda kike hidima ga al’umma, musamman ganin ke cikakkar almajira ce a gidan Malam Kabara. Wallahi wannan al’amari ya ba ni mamaki. Kuma na ji dadi a amtsayina na dan darikar kadiriyya. Daga Umar Hamidu Salka 08070762747

Mandela abin koyi ne
Mandela abin koyi ne ga shugabannin Afirka da ma na Duniya baki daya. Daga Amin Kaduna. 08092529913.

Ta’aziyar amarya
Assalamu alaikum. Don Allah Aminiya ku daure ku ba ni dama don nuna damuwata zuwa ga ’yan uwa da abokan arziki kan rasuwar amarya da ’yan tawagarta a sanadiyayr  hadarin mota. Allah Ya jikansu da rahama. Amin. Ango da mahaifin amarya ku yi hakuri. Daga Maryam  Abdulrasheed Jaji. 07032366792

Ta’aziyyar amarya
Assalam . Aminiya ina so ki mika min sakon ta’aziyyata ga iyayen amarya A’isha da kuma ango da fatan Allah Ya jikansu gaba daya. Amin. Daga Mami Abdullahi Kano. 08144469090.

Ta’aziyyar amarya Aisha
Assalamu alaikum Edita don Allah ka ba ni dama in mika ta’aziyyata ga iyaye da ’yan uwa da abokan arzikin su Aisha Adamu Bajoga. Allah Ya jikansu da rahama; Allah yasa in tamu ta zo mu cika da imani. Allah Ya kara mana imani. Allah Ya ba mu juriya da hakurin rashin su. Daga Maman  Innawuro, Tunga Minna. 07030891275.

Ga ’yan Najeriya
Kow ain ya tashi addu’a sai ya yi wa kansa, ya manta da matsalar kasarsa Najeriya, bayan muna bukatar addu’a mun kasa ganewa. To Allah Ka gyara mna, ta yadda za mu kai ko da rabin Saudiyya, a ci gaba da kwanciyar hankali da zaman lafiya. Daga Zainab Muhammad (Mami) Gombe 08062906565.

‘Yan mata a rage girman kai
Edita don Allah ka sanar wa ’yan amta a rage girman kai ko a samu mijin aure, saboda kudi ya hure muku kunne, duk da ana cewa maza suna da laifi, to na mata ya fi yawa. Daga yarinya ta gama ’yar makarantar sakandire, sai ta dauki girman kai ya fin a mai digiri. Ya kamata ku yi karatun t anatsu, ko kuma ku tsufa babu aure. Daga Masoyinku Yahaya Ahmed Jabo K/Hausa, Jigawa 08026392000.

 Shugabanni nagari
Mu ’yan arewa mafita Allah Ya zaba mana shugabanni nagari. Amin. Daga Habibu G. Yakubu Gwarzo 07055093659.

An kware wa PDP baya
Aminiya a lokacin da guguwar siyasa ta fara bugawa, an samu wasu daga cikin baragurbin ‘’yan  jam’iyyar PDP suna kware mata baya, to su sani fa mu ba mu damu da fitarsu ba. PDP ikon Allah ya kafata, kuma muna nan a matsayin babbar jam’iyyar  Afirka. Kuma Joanthan kamar ya ci zabe a 2015. Daga Alhaji Ali Baban Fati, Katsina 08170622330.

A yi koyi da Mandela
Salam Aminiyar jama’a ya kamata shugabannin Najeriya su koyi darasi daga Marigayi Nelson Mandela, gas hi dai ya mutu, amma farin jininsa kara karuwa yake kullum. Wai a Najeriya kuwa akwai shugaban da zai mutu mutanen kasar da ma na duniya su taru suna alhinin mutuwarsa? Ni dai nasan wani shugaban ko makotansa ba za su damu don ya mutu ba. Allah Ya kara taimakon Aminiya. Daga Rahama Umar Ramcy, Kano 07033245212.

Ga Sarkin Hadeja
Ina mika sakon gaisuwata ga Mai martaba Sarkin Hadeja, Alhaji Adamu Abubakar Maje (CON). Da fatan Allah Ya kara wa sarki lafiya. Daga Isah Ramin Hudu Hadeja. 08060353362

Hattara matasan Najeriya
Ina kira ga matasan Najeriya da su yi hattara da zaben 2015, idan kunne yaji, jiki ya sira. Daga Tijjani Ibrahim 08173956217.