✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutuwar aure ya kusa rusa rayuwata —Funke Akindele

A karon farko, Funke Akindele-Bello ta bayyana halin da ta shiga bayan mutuwar aurenta na farko.

A karon farko tauraruwar shahararren fim din barkwancin nan na Jenifa’s Diary, Funke Akindele, ta bayyana irin fadi-tashin da ta yi a lokacin aurenta da mijinta na farko kuma dan kasuwa, Kehinde Adeola Almaroof.

A wata tattaunawa da Chude Jideonwu (Chudeity) mai gabatar da shirye-shirye, Funke Akindele wadda aka fi sani da Jenifa, ta kuma bayyana yadda mutuwar auren nata na farko ya nemi ya ruguza rayuwarta.

Fitacciyar jarumar fina-finan Nollywood din, ta bayyana irin halin da ta shiga ne a lokacin da take shawartar mata da su guji hanzarin yin aure don kawai an matsa musu saboda ba su da aure ko don su shiga cikin tsara.

“Kada ku bari a matsa muku a kan yin aure. Ku yi aure don kuna so ku yi kuma kun shirya wa yin rayuwar aure, saboda akwai lokacin da kuruciya da kishi da kuma fushi za su taso, kuma ke ’yar Adam ce” a cewar Funke Akindele.

Funke, wadda mai shirya fina-finai ce, ta ce, “Ni a wancan lokacin kawai ina so ne in yi aure, ina so in yi abubuwa daidai, in samu ’ya’ya.

“Amma zaman auren bai yi dadi ba, daga karshe ma auren ya yi mummunan karshe a kafofin sa da zumunta, labarin ya watsu a ko’ina.

“Muna tsaka da daukar fim aka kira ni a waya aka shaida min abin da ke faruwa, lokacin sai da na ji kamar raina zai fita”.

Jenifa ta ce baya ga abin da ya faru da kuma halin tsananin damuwa da ta shiga daga baya, wasu manyan ayyuka da ta samu kuma sun nemi su kubuce mata a lokacin.

A cewarta, abin da ya fisshe ta shi ne ta ba ta karaya ba, sai ta yi ta kokarin kawar da tunanin abin daga zuciyarta, ta ci gaba da rayuwarta, ta sake tunkarar aikinta na  yin fina-finai gadan-gadan.

Ta kuma yi dace mahaifiyarta ta karfafa mata gwiwa kan ta ci gaba da rayuwarta da aikinta yadda ta saba.

Bayan mutuwar auren nata na farko, a 2016 Funke Akindele ta auri wani mawaki Abdulrasheed Bello kuma Allah Ya azurta su da tagwayen ’ya’ya.

A shekarar nan ta 2021 Funke da mijin nata suka yi bikin cika shekara biyar da aurensu.