✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutumin da ya yi ta dukan matarsa har ta mutu ya shiga hannu

Wani magidanci mai shekara 37 da ya yi ta dukan matarsa har ta mutu ya shiga hannu a jihar Ogun. A wata sanarwar da mai…

Wani magidanci mai shekara 37 da ya yi ta dukan matarsa har ta mutu ya shiga hannu a jihar Ogun.

A wata sanarwar da mai magana da yawun Rundunar ‘yan sandan jihar DSP Abimbola Oyeyemi, ya aikewa Aminiya ya shaida cewa jami’an rundunar sun kame Mutiu Sonola, wanda ake zargi da kashe matarsa Zainab Shotayo a jiya Laraba bayan da mahaifinta ya kai kararsa ga ‘yan sanda.

Ya ce, Mahaifin marigayiyar ya shaida cewa wanda ake zargin ya dade yana jibgar matarsa a duk lokacin da dan sabani ya shiga tsakanin su, ya ce ana ci gaba da bincike akan wanda ake zargin kana za a gabatar da shi a gaban kotu.

Mutiu Sonola