Dubbun wani mutum mai shekara 32 da ya kitsa yin garkuwa da kansa domin karbar kudin fansa har Naira dubu 500 ta cika a Jihar Gombe.
Rundunar ’yan sandan Jihar Gombe ce ta cafke matashin mai suna Halliru Umar wanda mazaunin Unguwar Tudun Wada da ke jihar.
A shekarar 2021 da ta gabata ce mutumin ya hada baki da wani abokinsa domin shirya garkuwa da kansa da zummar karbar kudin fansa har Naira dubu 500 a hannun wata ’yarsa mai suna Zainab Umar.
Halliru Umar, ya shirya garkuwa da kansa ne ta hanyar cin amanar sirikar ’yarsa wacce ta bashi tukin Keke Napep ya ke haya a lokacin da jarinsa na kasuwanci ya durkushe.
Sai dai bayanai sun ce mutumin daga baya ya sayar da Keke Napep din a kan kudi N250,000 ba tare da sanin sirikar ta shi ba.
Da yake gabatar da wadanda ake zargin a hedikwatar ’yan sandan jihar, Kwamishinan ’yan sanda Ishola Babatunde Babaita, ya ce bayan mutumin da ya gaza mayar wa da sirikarsa dukiyarta da ta nema, ya hada baki da wani mai suna Ahmed Landa, inda suka shirya garkuwa da shi ta bogi domin karbar kudin fansa a hannun yarsa da zummar samun damar mayar wa da sirikarsa dukiyarta.
SP Marry Obed Malum, kakakin ’yan sandan jihar da ta yi jawabi a madadin Kwamishinan ’yan sandan, ta ce daga cikin hanyoyin da ababen zargin biyu suka yi amfani da su wajen kitsa garkuwar ta bogi har da barazanar kisa muddin aka gaza biyan kudin fansar na Naira dubu 500 da suka nema.
Duk da cewa mutumin da ya shiga hannu bai kore tuhumar da ake masa ba a yayin da ’yan sandasuka titsiye shi, sai dai Kwamishinan ya ce a na ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin kuma da zarar sun kammla za su tura masu laifin zuwa kotu.
Kwamishinan ya kuma ja hankalin al’umma da su rika zama a ankare wajen sanya idanu kan duk wasu lamurra da ke faruwa a zamantakewarsu, sannan su rika mika rahoton duk wani motsi da basu yarda da shi ga ’yan sanda ko wata hukuma mafi kusa da su.