✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutumin da ya siyar da dansa da matarsa ya shiga hannu

Ya siyar da matarsa kan Naira 1,400,000, da kuma dansu kan Naira 600,000.

Wani matashi mai suna Kingsley Essien mai shekaru 36 ya shiga komar ‘yan sanda bisa zargin siyar da matarsa Bright Essien kan Naira 1,400,000, da kuma dansu kan Naira 600,000.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihad Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi ne ya bayyana hakan da cewa sun kamo Kingsley ne bayan matarsa Bright ta shigar da kara a babban ofishinsu da ke Agbara.

“Bright ta shigar da kara gurinmu a watan Oktoban 2021, inda ta ce mijinta Kingsley ya sanar da ita cewa ya samar mata aiki a Bamako da ke kasar Mali inda ya saba samowa mutane aiki kuma suna samun alheri sosai,” in ji shi.

“Ta bayyana cewa kasancewarsa mijinta ya sa ba kawo komai a ranta ba har sai da ta je Malin sannan ta ga ashe siyar da ita yayi ga wasu guggun masu safarar bil Adama domin karuwanci da wata mata ke jagoranta kan naira 1,400,000,” a cewar Oyeyemi.

Kakakin ya kuma ce karshe dai ta yi nasarar dawowa gida ne bayan ta nemi taimakon Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Bamako.

Dawowarta ke da wuya ta lalubi dansu mai shekaru biyu da ta bari a gida tare da mijin nata ta rasa, take ta kai kara ofishin ’yan sanda da ke Agbara, inda DPO Abiodun Salau ya tashi tawagar bincike ta kamo mijin nata.

Kazalika rundunar ta ce binciken ne ya kai mijin ga bayyana siyar da dan nasu kan naira 600,000, kuma take Kwamishinan ’yan sanda Lanre Bonkole ya ba da umarnin kamo wanda ya siya yaron.