✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum ya rasa matsayinsa a gaban Allah

Allah Yana da kyakkyawan shiri domin jin dadin mutum, kafin mutum ya yi wa Allah taurin kai ta wurin kin bin umarnin da Allah Ya…

Allah Yana da kyakkyawan shiri domin jin dadin mutum, kafin mutum ya yi wa Allah taurin kai ta wurin kin bin umarnin da Allah Ya ba shi. Kyakkyawan shiri wadda Allah Ya yi wa mutum ya kunshi:

Mutum ya rasa masarautarsa. “Kuma Allah Ya ce, bari Mu yi mutum cikin surarmu, cikin kamaninmu: su yi mulki kuma bisa kifaye na teku, da tsuntsaye na sama, da bisashe, da kuma bisa dukan duniya, da kowane abu mai rarrafe a bisa kasa, Allah fa Ya halitta mutum cikin suratasa, cikin surar Allah Ya halice shi, namiji da ta mace Ya halicce su.” (Farawa 1 : 26 – 27). Allah Shi ne Mai mulki a cikin sama da duniya duka, amma da Ya halicci mutum, sai Ya yarda ya ba mutum ’yancin sarauta a bisa dukan abin da Shi Allah Ya halita, har bisa Iblis/Shaidan, domin shi ma halitar Allah ne, wannan ya nuna cewa a cikin dukan halitar Allah babu wadda ya fi mutum daraja a gabanSa. Shi ya sa, Allah Ya zabe shi, Ya kuma damka masa wannan amana ta rike wannan duniya da duk abin da ke cikinta a hannunsa; wannan kafin mutum ya yi zunubi ne. Da zarar mutum ya aikata zunubi, sai Allah Ya janye wancan gatan da ya ba shi. Yau Shaidan ya kwace mulkin duniyar nan daga hannun mutum, shi ya sa, abin da yake so ne kawai za a yi musamman ga wadanda ba sa jin tsoron Allah. Idan muka lura da rayuwar yau da kullum, daga halayen mutane zuwa ayyukansu, yawancin lokaci abubuwa ne da Allah Yana kyamar ganinsu, kisa da sata da fasikanci da zina da husuma da kiyayya da cin amana da maita da zalunci da danne hakkin mutane da sauransu su ake yi. Wadansu abubuwan suna cewa wayewa ne, ka ga saurayi ya sa wando amma duwawunsa a waje, ko kuwa budurwa ta sa riga amma rabin nononta na waje kuma ko kunya babu: cewa suke yi zamani ne; duk irin wannan abu aikin Iblis ne, kuma domin ya rigaya ya karbi mulkin wannan duniya daga hannun wanda Allah Ya ba tun farko. Wannan ba karamin asara ba ne ga mutum. Mutum da ya kamata ya yi mulki, amma yau shi ne bawa; ana mulkinsa, wannan abin kaito ne. Littafi Mai tsarki yana koya mana cewa “Adalci yakan daukaka al’umma: Amma zunubi abin zargi ne ga dukan dangogi.” (Misalai 14 : 34). Mu sani cewa ko a yau, zunubi, zunubi ne; bai canja kamanni a gaban Allah, karshen aikata zunubi mutuwa ne kuma da kunya, ko a nan duniya ko kuwa a gaban Allah lokacin shari’arSa, a wancan lokaci babu wadda ya isa ya guje ko ya buya daga gabansa, a wannan zamani muna ganin yadda shugabanni da masu mulki ke satar kudin da zai amfani jama’ar kasa gaba daya, ko jiha, ko karamar hukuma, su boye domin amfanin kansu kawai da mai-yiwuwa danginsu; idan hukuma tana so ta kama su, sai su guje su bar kasar su tafi wata kasa inda suke zaton ba za a same su ba, suna tsammanin idan mutum ya manta shi ke nan ya zama rabonsu, sun manta akwai Allah wanda ba Ya mantuwa, kuma Mai adalci ne Shi, shari’a a bisa gaskiya Yake: babu mutum guda wanda ya isa ya guje maSa.
An taba ba ni labarin wani mai kudi a wannan kasa wanda ya ce da ya sha kunya a gaban mutane, gwamma ya fuskanci shari’ar Allah. Bai san wannan Allah da muke magana a kanSa ba, lokacin idanunsa za su budu, a lokacin ne zai ce da-na-sani. Mutane da yawa za su yi wannan kukan ba domin ba su san gaskiya ba, amma domin sun bijire ga gaskiya, sun ki bin tafarkin Ubangiji Allah, sun fi son duniya da abin da duniya za ta ba su.
Kai dan uwana; bari in yi maka tambaya, mene ne kake fafara a wannan duniya? Kudi ne ko fasikanci da sauransu? A yau akwai masu bauta wa kudi, ya riga ya mallake zuciyarsu, shi ya sa za su iya kashe mutum dan uwan su muddin ta dalilin kisan za su samu kudin nan. Idan abin da kake da shi ba ta hanyar da ya dace a gaban Allah ne ka same su ba, to ba shakka akwai hadari a gabanka ko gabanki. Mene ne ke mulki cikin rayuwarka? Allah ne ko kana karkashin ikon Shaidan?
Mutum ya rasa muhallinsa:
Lokacin da Allah Ya halitta mutum, Ya shirya masa wurin zama a cikin gonar Adnin: “Ubangiji Allah kuma Ya sifanta mutum daga turbayar kasa, Ya hura masa numfashin rai cikin hancinsa; mutum kuma ya zama rayayyen mai rai. Ubangiji Allah kuma Ya dasa gona daga wajen gabas, a cikin Adnin, can kuwa Ya sanya mutumin da ya sifanta.” (Farawa 2: 7 – 8). Yadda Allah Ya shirya wa mutum wajen zamansa ke nan. Zunubi ya sa aka kore shi daga cikin gonar. “Kuma Ubangiji Allah Ya ce, ga shi mutumin ya zama kamar daya daga cikinmu, mai sanin nagarta da mugunta, yanzu fa, kada ya mika hannunsa, ya dauka kuma daga itace na rai ya ci, ya yi rai na har abada: Ubangiji Allah fa Ya fishe shi daga gonar Adnin, shi nome kasa inda aka dauke shi. Ya fa kore mutumin; a gabashin gonar Adnin kuma Ya sanya Cerubim da takobi mai harshen wuta mai juyawa a kowace fuska, domin a tsare hanyar itace na rai.” (Farawa 3: 22 – 24). Allah Ya kore shi daga inda aka yi masa shiri tun farko, ya zama dole ya samu wurin da zai fake da matarsa. Rashin biyayya ne ya kawo wannan matsala. Har yau daya daga cikin damuwar dan Adam shi ne muhalli. Kowa yana neman koda bukka ne ma shi da iyalinsa su iya zama a ciki. daya daga cikin wahalolin da zunubi ya kawo ga dan Adam.
Mutum ya rasa hanyar samun abinci a sauwake. Abinci ba abu ne wanda ya kamata ya sha wahala kafin ya samu ya ci ba, Allah Ya rigaya ya shirya wa mutum abin zai ci domin ya rayu da shi, “Sai Ubangiji Allah Ya dauki mutum, ya sanya shi cikin gonar Adnin domin shi aikace ta, shi tsare ta kuma. Ubangiji Allah kuma Ya dokace mutumin, Yana cewa, an yarda maka ka ci daga itacen gona a sake: amma daga itace na sanin nagarta da mugunta ba za ka diba ba ka ci: cikin rana da ka ci, mutuwa za ka yi lallai.” (Farawa 2: 15 – 17).
Zunubi ya kawo la’ana a kan mutum, ga abin da ya faru wanda ya sa mutum cikin wannan wahala. “Kuma ya ce ga Adamu, don ka lura da muryar matarka, har ka ci kuma daga cikin itacen, wanda Na dokace ka, cewa, ba za ka ci shi ba; sabili da kai an la’anta kasa; da wahala za ka ci daga cikinta duk muddar ranka; kayayuwa da sarkakiya za ta haifa maka; ganyen saura kuma za ka ci; sai da jibi a fuskarka za ka ci abinci, har kuma ka koma kasa; gama daga cikinta aka ciro ka: gama turbaya ce kai, ga turbaya za ka koma.” (Farawa 3: 17 – 19). Samun abinci a yau, ba abu ne mai sauki ba ko kadan; sai ka yi zufar nan da Allah Ya ambata.
Mu ci gaba da yin addu’a domin salama ta tabbata a kasarmu. Za mu ci gaba idan muna cikin masu rai mako na gaba, Allah Ya albarkace mu duka, amin.