✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum uku sun mutu a rushewar gini

An hako gawar wata jami’ar dan sanda da wasu mutum biyu daga baraguzan wani bene da ya rushe a yankin Lagos Island na jihar Legas.…

An hako gawar wata jami’ar dan sanda da wasu mutum biyu daga baraguzan wani bene da ya rushe a yankin Lagos Island na jihar Legas.

Benen mai hawa uku ya rushe ne da misalin 3.00 na dare a layin Freeman, inda ya fado a kan wasu mutum 12 daga cikin mazaunansa.

Masu aikin ceto da suka hako gawarwakin sun ce sun gano ‘yar sandar ce a kusa da kofar ginin, wanda ke nuna ya fado mata ne a lokacin da take kokarin fita domin tsira da rayuwarta.

“Gaba daya an ceto mutum biyu an kuma ceto wasu takwas”, inji jami’in hukumar agaji ta kasa (NEMAN) mai kula da Kudu maso Yammacin Najeriya Ibrahim Farinloye, wanda ya ce daya daga cikin mamatan yaro ne.

Ya yi bayanin ne kafin adadin mamatan ya karu.

Daga cikin wadanda aka ceto mutum daya ya galabaita an kuma garzaya da shi asibiti, a cewar jami’an hukumar agajin NEMA da na jihar Legas (LASEMA) da ‘yan sanda da ke aikin ceton.

Tun da farko Aminiya ta ambato Ibrahim Farinloye na tabbatar da an kubutar da wasu mutum shida daga baraguzan ginin.

Site of the collapsed building
Site of the collapsed building